Saboda kiyayyar da ake nunawa addinin Musulunci yasa Charlotte ta karbi kalmar shahada

Saboda kiyayyar da ake nunawa addinin Musulunci yasa Charlotte ta karbi kalmar shahada

- Wata budurwa ta karbi addinin Musulunci bayan ta gabatar da kwakkwaran bincike akan shi saboda yanayin yadda taga duniya na nuna kyama a kanshi

- Budurwar mai suna Charlotte ta taso a cikin Musulmai amma hakan bai taba sawa tayi tunanin ta Musulunta ba, har sai da taga yadda duniya ke nuna kiyayya akan addinin sannan ta fara gabatar da bincike

- Charlotte tayi rayuwa a kasashe kusan guda shida na duniya, hakan yasa taga Musulmai kala-kala da akida daban-daban, kuma akasarin abokananta kusan duk Musulmai ne

Musulunci shine addinin da yafi kowanne yaduwa da rinjaye a duniya, akwai dalilai da dama da suka sanya, amma muhimmin ciki shine yadda wadanda ba Musulmai ba suke komawa Musulunci.

A wannan karon mun samo labarin wata kyakkyawar budurwa wacce ita kuma na ta labarin daban yake dana kowa. Duk da dai akwai Musulmai a yankin da take, amma ta shigo addinin bayan ta gabatar da wani bincike.

Saboda kiyayyar da ake nunawa addinin Musulunci yasa Charlotte ta karbi kalmar shahada
Saboda kiyayyar da ake nunawa addinin Musulunci yasa Charlotte ta karbi kalmar shahada
Asali: Facebook

Charlotte kyakkyawar budurwa ‘yar shekara 25 daga kasar Belgium. Ta shigo addinin Musulunci bayan fitar ta daga addinin Kiristanci. Ta girma a kasashe guda 6 na duniya, sannan ta ga Musulmai kala-kala da akida kowa da tashi.

Charlotte tana da abokanai Musulmai masu yawa kuma suna da mutunci suna kula da ita sosai. Haka kuma ita ma tana jin dadin mu’amala da su saboda basu nuna mata wariya.

Musulmai ne amma basu nuna hakan, sun dauki kansu kamar kowa. Charlotte ta san cewa su Musulmai ne amma hakan bai dame ta ba. Tunda su basu damu suyi zancen addini da ita ba, duk abinda ta koya akan addinin Musulunci ta koya ta yanar gizo ne.

Bata damu da wani addinin Musulunci ba har sai da taga kyamar da ake nunawa addinin tayi yawa ga Musulmai.

KU KARANTA: Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya

Wannan kyama da ake nunawa Musuluncin ya sanya mata wasi-wasi a cikin zuciya, inda ta fara neman yadda za ta kara samun ilimi akan addinin Musulunci, tana so ta kare abokananta a idon duniya.

Tunda abokananta basu damu da yi mata zancen addini ba, kuma ita ma bata so ta tambaya, kawai sai ta shiga yanar gizo ta fara bincike. Ta samu Qur’ani ta fara karantawa. Bata taba tunanin cewa hakan zai kawo canji a rayuwarta ba.

Ta fara karanta Qur’ani tare da tarihin addinin Musulunci, wanda ta bayyana shi akan abinda yafi bude mata ido a rayuwa, ya kuma canja mata rayuwa baki daya.

“Naji dadi matuka da abinda na koya, yadda kyakkyawan addinin Musulunci yake, yadda yake bawa mutane nutsuwa,” cewar Charlotte. Bayan tayi karatu mai nisa akan Musulunci ta samu kwanciyar hankali sosai da shi sai ta ce: “Ina so na zama Musulma.” Hakan ya sanya ta karbi kalmar shahada.

Kafin ta karbi Musulunci Charlotte na fama da matsaloli na rayuwa da suka shafe ta, amma bayan ta karbi addinin duka matsalolinta sun kau. “Musulunci ya taimakeni na tsaya da kafa ta a lokacin da nake ganin bani da wani karfi. Na samu karfin guiwa da kwanciyar hankali,” cewar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng