Kotu ta yanke hukunci a shari’ar Ali Sanda Konduga da Hukumar DSS

Kotu ta yanke hukunci a shari’ar Ali Sanda Konduga da Hukumar DSS

Tsohon kakakin ‘yan kungiyar ta’addan Boko Haram, Ali Sanda Konduga, ya gaza samun biyan bukata a karar da ya kai hukumar tsaro ta DSS a gaban babban kotun tarayya.

Ali Sanda Konduga ya bukaci Alkalin kotun tarayya na Abuja ya kama jami’an DSS da laifin tsare shi a hannunsu ba tare da samun cikakken izni kamar yadda doka ta tanada ba.

Konduga wanda ya kasance Mai magana da yawun bakin ‘Yan Boko Haram ya kai kara a kotu ya na tuhumar DSS da keta masa hakkinsa a sakamakon garkame shi da su ka yi.

Kamar yadda mu ka samu labari, Sanda Konduga wanda aka taba tsarewa ya bukaci kotu ta umarci hukumar DSS ta biya shi Naira miliyan 500 da sunan ci masa mutunci.

Sai dai a shari’ar da aka yi a Ranar Litinin, 2 ga Watan Maris, a babban kotun na Abuja, Mai shari’a Anwuli Chikere ya yi fatali da rokon da Lauyan Sadiq Konduga ya gabatar masa.

KU KARANTA: Rigimar gida ta fara cin Sojojin Boko Haram - Rahotanni

Lauyan da ke kare ‘Dan ta’addan, Emmanuel Edu, ya bayyana cewa bai ji dadin wannan hukunci da aka yi ba. Edu ya ce an cigaba da tsare Konduga bayan wa’adin kasonsa ya cika.

“Ya kamata ace an sake shi bayan shekaru uku, amma aka cigaba da tsare shi na wasu shekaru ukun kafin a sake shi. Don haka hakkinsa ya ke nema a kotu.” Inji Barista Edu.

Lauyan ya kara da cewa: “A wuri irin Najeriya, abin da ake bukata shi ne adalci har ga wanda ya yi laifi. Akwai hukuncun daurin gidan yarin da ake yankewa kowane laifi.”

An daure Konduga a gidan yari ne bayan an same shi da laifin ta’addanci a shekarar 2011. Amma DSS masu fararen kaya ba su sake shi ko da lokacin zamansa a kurkuku ya cika ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel