Dan takarar APC ya janye daga zaben maye gurbi da za a yi a Sokoto, ya ce a zabi PDP

Dan takarar APC ya janye daga zaben maye gurbi da za a yi a Sokoto, ya ce a zabi PDP

Abubakar Bello Umar, dan takarar jam'iyyar APC a zaben maye gurbi na ranar 14 ga watan Maris a mazabar Kebbe, jihar Sokoto, ya janye takararsa.

"Bayan na tuntubi iyayena, dattijai, abokai, masoya da magoya baya, ina mai sanar da janyewa daga takarar da nake yi, na janye ne bisa radin kaina, ba tare da fuskantar takura ko barazana ba," a cewarsa.

Sannan ya kara da cewa, "ina son jama'a su sani cewa na janye saboda son cigaban yankinmu da kuma bawa maslaha fifiko."

Kazalika, Umar ya bukaci magoya bayansa su zabi dan takarar jam'iyyar PDP, Abubakar Adamu Kebbe.

"Kamar yadda ku ka sani, al'adar siyasar mu ce a Kebbe mu rungumi sulhu tare jingine banbancin siyasa domin goyon bayan dan takara guda daya.

"Mun fi mayar da hankali ne a kan cigaban karamar hukumar mu ba siyasa kawai ba," a cewarsa.

Za a gudanar da zaben maye gurbi a mazabar Kebbe ne biyo bayan mutuwar tsohon wakilin karamar hukumar a majalisar dokokin jihar Sokoto a cikin watan Disamba na shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel