Uwar da ta durkusa ta haifeni wallahi karuwa ce - Cewar dan gidan Kemi Olunloyo

Uwar da ta durkusa ta haifeni wallahi karuwa ce - Cewar dan gidan Kemi Olunloyo

- Wani abun mamaki da daure kai da ya faru a 'yan kwanakin nan ya daurewa mutane da yawa kai, musamman idan aka yi tunani irin na soyayyar dake tsakanin uwa da danta

- Wannan lamari ya faru ne ta inda dan ya fito kafar sadarwa ta zamani ya wallafa cewa uwar da ta tsugunna ta haife shi karuwa ce, har yake bayar da hujja da irin mazan da take kwanciya

- To sai dai kuma an bayyana cewa dama can mahaifiyar ta sallamawa dan, domin sun rabu shekaru da jimawa, inda har yake zargin ta da shirin kashe shi da rake kokarin yi, ga dai cikakken labarin a kasa

Fitacciyar ‘yar jarida mai jawo kace-nace a yanar gizo, Kemi Olunloyo, dan data haifa da cikinta ya kirata da karuwa a ranar da ya cika shekaru 33 da haihuwa.

A rubutun da ya wallafa. dan gidan Kemi Olunloyo da ya sanya sunansa da Eni a shafinsa na Instagram, alamu sun nuna cewa tuni dai mahaifiyar tashi dama ta sallama mishi tunda a rubutun nashi ya kirata da ‘mahaifiyata a da’.

Uwar da ta durkusa ta haifeni wallahi karuwa ce - Cewar dan gidan Kemi Olunloyo
Uwar da ta durkusa ta haifeni wallahi karuwa ce - Cewar dan gidan Kemi Olunloyo
Asali: Facebook

Ya ce mahaifiyata a da Kemi Olunloyo, tana abubuwa da yawa da basu dace ba ga mutane. Haka kuma a cikin rubutun nasa ya kirata da karuwa.

Ga dai abinda ya rubuta a shafin nasa:

“Wannan shine labari na bayan shekara daya. Mahaifiyata ko kuma nace tsohuwar mahaifiyata ki daina turo mini sakon murnar ranar haihuwa. Bayan shekarar da ta gabata mun samu sabani ta waya inda take gayawa ‘yan iskan ‘yan Najeriyan nan su taya ni murnar ranar haihuwa. Ni kuma ban ma san su ba.

“Duk saboda ita ne, da ace ta rufe bakinta duk haka ba zai faru ba, yanzu ga abinda tayi? Tana gayawa mutane karya. Musamman ma ba ta da mutunci ba ‘yar arziki ba ce. Abinda ta sani kawai shine tayi amfani dani da ‘yan uwana a matsayin abubuwan wasa domin ta samu abinda take so.

KU KARANTA: Kasar Argentina ta zama kasa ta farko a duniya da ta halatta zubar da ciki

“Yanzu na sani kwarai tana yin wasu abubuwan domin ta cutar da wasu mutanen da kuma ni, saboda kowa yana so ya zama abokinta.

“Hakan ya saka ta zama karuwa, tana zuwa tana kwanciya da maza kala-kala domin ta samu cikin shege. Hakan na faruwa tun ina tare da ita. Bayan ta kore ni ta nemi hanyar da za ta kashe ni. Amma wani abin mamaki har yanzu gani lafiyata lau. Kuma babu abinda zai same ni mutukar ina raye, kuma Allah zai kare ni. Wannan shine takaitaccen labari na.”

‘Yan Najeriya dai sun yi caa akan wannan rubutu da ya wallafa, inda kowa ke fadar albarkacin bakinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel