Tsananin talauci yasa matarshi ta gujeshi ta barshi da 'ya'ya 7, sai ga Baturiya ta zo ta aure abin ta
- Wai dama Hausawa sun ce rabo na Minallahi, tsuntsu daga sama gasasshe, kamar yadda Allah ya kawo wani mutumi mata zankadediya daga kasar Canada
- Ita dai wannan mata ta zo kauyen su mutumin ne a yawon da take yi na bude indo yayin da ta taso daga kasarta ta Canada, sai dai tana zuwa kauyen nan sai Allah ya sanya mata soyayyar wannan mutumi
- Bayan yi mata bayani akan halin da yake ciki, Baturiyar ta sha alwashin daukar nauyinsa dana 'ya'yansa zuwa kasar Canada domin su cigaba da rayuwa a can
Wasu hotunan biki na wata Baturiya da wani mutumi dan nahiyar Afrika wanda yake da ‘ya’ya guda bakwai ya bazu a shafukan sadarwa na yanar gizo.

Asali: Facebook
Yadda labarin ya bayyana shine, mutumin yana da ‘ya’ya guda bakwai, ita kuma Baturiyar ta zo yawon bude ido ne Afrika.
A cewar wani mai amfani da dandalin sada zumunta na Twitter mai suna @PH_Promoter, mutumin matar shi ta gudu ta barshi da yara guda bakwai saboda tsananin talaucin shi.
KU KARANTA: Kotu ta saki wani dan fashi mata-maza don rashin ma'adanarsa a gidan yari
Sai dai wani abin mamaki shine, tana guduwa sai wannan Baturiya ta ziyarci kauyen kuma ta kamu da soyayyar wannan mutumi.
A karshe sun yi aure, kuma Baturiyar ta dauki nauyin daukar su duka domin tafiya da su kasar Canada su cigaba da zama a can.

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng