Kudin aure nake nema shi yasa na shiga fashi da makami - Matashi Shehu Abdullahi

Kudin aure nake nema shi yasa na shiga fashi da makami - Matashi Shehu Abdullahi

- A yayin da kowanne saurayi yake so yayi aure wanda zai zame masa abin alfahari a rayuwa kuma ya zamewa 'ya'yanshi abin alfahari

- Sai ga wani matashi ya fada harkar da a karshe ta kai shi ga shiga komar 'yan sanda duka akan neman kudin aure

- Saurayin mai suna Shehu Abdullahi da abokanan shi guda biyu an cafke su akan babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri a jihar Bauchi, inda suka addabi matafiya da fashi da mamaki

Wasu mutane uku da aka kama, Shehu Abdullahi, mai shekaru 20; Babawuro Jauro Sani, mai shekaru 27 da kuma Wada Wakili Musa, mai shekaru 25, ‘yan sanda sun samu nasarar cafke su, inda yanzu ake shirin gabatar da su a gaban kotu.

Duka samarin guda uku ‘yan sanda ne suka cafke su a jihar Bauchi, bayan sun kama su da laifin fashi da makami.

Kudin aure nake nema shi yasa na shiga fashi da makami - Matashi Shehu Abdullahi

Kudin aure nake nema shi yasa na shiga fashi da makami - Matashi Shehu Abdullahi
Source: Facebook

Samarin sun addabi mutanen yankin dake bin babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano.

KU KARANTA: Auren mace fiye da daya ya fi bibiyar matan banza - Binta ta shawarci maza

A yadda rahoto ya nuna, mutanen guda uku sun rufe babbar hanyar, abinda ya sanya zirga-zirga ta tsaya cak a hanyar, sai suka fara kai wa mutane hari babu gaira babu dalili.

Shehu Abdullahi wanda yake shine karamin cikinsu ya bayyana duka yadda suke gabatar da ta’asar tasu, inda ya bayyana cewa ya shiga wannan harkane saboda yana so ya samu kudin da zai biya sadakin aure.

“Zancen gaskiya shine, ina so nayi aure amma bani da kudi. Haka yasa na shiga domin na samu kudin da zanyi aure.”

A Najeriya dai matsalar rashin aikin yi ta tilasta wasu mutanen da yawa shiga ayyukan ta'addanci da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu da dai sauransu.

Duk da cewa gwamnati nayin iya bakin kokarinta wajen ganin ta kawo karshen wannan lamura amma abin ya gagara, inda a kowacce rana ake kama sababbin masu laifi a fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel