Shugaba Buhari zai karbo duk kudin Najeriya da aka boye a ketare - Malami

Shugaba Buhari zai karbo duk kudin Najeriya da aka boye a ketare - Malami

Abubakar Malami, wanda shi ne Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin Najeriya ya ce gwamnati za ta dage wajen karbe dukiyar Najeriya da aka kai waje.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta huta ba, har sai ta ga ta karbe duk kudin Talakawan Najeriya da aka sace daga asusu, aka boye a kasashen waje.

Abubakar Malami SAN ya kuma nuna cewa gwamnatin da shugaba Muhammadu Buhari ya ke jagoranta ta hada-kai da hukukomi domin dawowa kasar da kudinta.

Ya ce: “A ketare, gwamnatin Najeriya ta na aiki da hukumomi da-dama domin ta gano, sannan ta dawo da kudin da aka sace daga nan aka boye su a wajen Najeriya.”

“Ana cigaba da yunkurin dawo da kudin Najeriya da aka sace. Gwamnatin tarayya a karkashin shugaba Muhammadu Buhari ba za ta dagawa wani Barawo kafa ba.”

KU KARANTA: Buhari ya yi magana game da kisan kiyashin da aka yi a Kaduna

Shugaba Buhari zai karbo duk kudin Najeriya da aka boye a ketare - Malami
Malami ya ce Najeriya za ta dawo da kudin da aka sace
Asali: Depositphotos

Abubakar Malami ya nuna cewa duk wani Mutumi ko kamfani da ya sace kudi daga asusun Najeriya, ya boye a bankunan waje, sai ya dawowa kasar da dukiyarta.

Malami ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi magana wajen wani biki da ‘Daliban jihar Kebbi da ke karantar ilmin shari’a a Jami’a su ka shirya a Birnin Kebbi.

“Daga cikin yakin da ake yi akwai batun kawo dokoki da gyara tsare-tsare da kuma kawo hanyoyin rigakafin hana sata da karbo dukiyar sata.” Inji Malami SAN.

Idan ba ku manta ba, mun kawo maku labari daga Jaridar Daily Trust cewa gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, ya yi jawabi a taron, inda ya yabawa kokarin gwamnati.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel