Buhari ya yi magana game da kisan gillar da yan bindiga suka yi a Kaduna

Buhari ya yi magana game da kisan gillar da yan bindiga suka yi a Kaduna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bacin ransa bisa mummunar harin kisan kiyashi da wasu yan bindiga suka kai ma al’ummar jahar Kaduna a ranar Lahadi inda suka kashe sama da mutane 51.

Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne ta bakin hadiminsa a bangaren watsa labaru, Malam Garba Shehu a ranar Litinin, wanda ya ce ta tabbata yan bindigan suna kai ma jama’an da ba su ji, ba su gani ba hari sakamakon matsin lamba da suke fama da ita daga wajen jami’an tsaro a dajin Birnin Gwari da Kaduru.

KU KARANTA: Majalisa ta haramta ma Buhari kashe kudaden Abacha a titin Abuja zuwa Kano

“Gwamnatin nan ba za ta saurara ma yan bindiga da miyagun mutane ba, musamman a kokarin da take yi na sakar musu Sojoji dake farautarsu ruwa a jallo, don haka ina tabbatar ma jama’an Kaduna da kuma na sauran yankunan jahar da cewa gwamnatinmu za ta yi amfani da duk wata dama da take da shi don kawo karshen yan bindiga.

“Ya kamata miyagun nan su sani babu yadda za’a yi su cigaba da cutar da jama’a ba tare da sun gamu da fushin gwamnati ba, musamman gwamnatin da jama’a suka zabe ta domin ta kare rayukansu da dukiyoyinsu.” Inji sanarwar.

Bugu da kari, shugaba Buhari ya jajanta ma al’ummomin da hare haren suka shafa, sa’annan ya taya su alhinin asarar da suka yi, amma daga karshe ya ce:

“Miyagun nan ba za su yi ta samun sa’a a kullum ba, a shirye mu ke mu karya su, kuma duk tsawon lokacin da za su dauka sun tserewa ko suna buya, sai mun bankado su, kuma mun hukunta su.” Inji shi.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya yi alkawarin share duk wasu yan bindiga dake jahar Kaduna daga doron kasa biyo bayan wani mummunan hari da suka kai a ranar Lahadi inda suka kashe mutane 51.

Miyagun yan bindiga sun kai mummunar hari a ranar Lahadi, 1 ga watan Maris inda suka kashe mutane da dama a kananan hukumomin Igabi da Giwa, sa’annan suka kona gidaje da motoci da dama.

Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya yi kama da harin ramuwar gayya sakamakon yan bindigan suna zargin al’ummomin yankunan da suka kai ma hari da baiwa jami’an tsaro bayanan sirri game da ayyukansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel