Coronavirus: Mutane 80,000 sun kamu a kasar Sin, 4,000 a kasar Koriya ta kudu

Coronavirus: Mutane 80,000 sun kamu a kasar Sin, 4,000 a kasar Koriya ta kudu

Rahoto daga kasar Sin ya nuna cewa an samu karin mutane 202 wadanda suka kamu da cutar coronavirus da 42 na wadanda suka rasa rayukansu wadda ya kai adadin na masu dauke da cutar a birnin kasar Sin 80,026.

A halin yanzu, cibiyar taikaita yaduwar cututtuka ta kasar Koriya ta bayyana cewa, kasar Koriya ta kudu ta samu karin 476 na sabbin wadanda suka kamu da cutar wadda ya kai adadin na wadanda suke dauke da coronavirus 4,212.

Yawan adadin wadanda cutar ta kashe a birnin kasar Sin ya kai kimanin 2,919 cewar hukumar kiwon lafiya ta kasar, yayinda aka samu wasu 4 da suka rasa rayukansu a kasar Koriya ta kudu, kuma adadin wadanda suka rasa rayukansu ya kai 22 a kasar.

A kasar Sin, an ruwaito cewe fiye da rabin wadanda suka kamu da cutar sun warke .

Bullowar cutar a kasar Koriya ta kudu, inda itace mafi girma bayan Kasar Sin da cutar ta fara yaduwa a watan Disamba 2019.

An samu rahoto cewa, tafi yaduwa a kudu maso gabas na birnin Daegu da kuma kewayen arewacin Gyeongsang.

Yayinda cutar take takaituwa da sannu a kasar Sin, an samu rahoto cewa, cutar tayi tashin gwauron zabi da kashi hamsin cikin dari a wurare kamar kasar Koriya ta kudu da Kasar Italiya.

A bangare guda, Kasar Tunisiya da da kasar Senegal sun tabbatar da bullar cutar Coronavirus na farko, hakan ya ya kai adadin kasashen da ta bulla a nahiyar Afrika biyar.

Gabanin shigarta kasashen nan biyu a yau Litinin, kasashen Misra, Algeria, da Najeriya sun tabbatar da bullar cutar da ta hallaka akalla mutane 3000 a fadin duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel