'Ka kasa cika alkawari': fusataccen mutum ya katse gwamna Badaru yana cikin lissafo aiyuka a bainar jama'a

'Ka kasa cika alkawari': fusataccen mutum ya katse gwamna Badaru yana cikin lissafo aiyuka a bainar jama'a

Wani fusataccen mutum a ranar Asabar ya tari numfashin Gwamna Muhammadu Badaru na jihar Jigawa a zarginsa da yayi da rashin kammala asibiti da titunan jihar a karamar hukumar Birnin Kudu.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, Gwamnan ya je karamar hukumar ne don kaddamar da cibiyar tallafin ilimi wacce dan majalisa Magaji Aliyu ya ba wa dalibai 5,000 na jihar.

A kan mumbari, Badaru na cikin lissafo aiyukan gwamnatin tarayya a jihar Jigawa din ne lokacin da fusataccen mutumin ya katse shi.

Muryar mutumin da aka kasa ganewa ta bayyana ne daga cikin taron mutanen inda ya ke cewa: "Aikin titin da ka yi mana alkawari da kuma asibitin karamar hukumar Birnin Kudu duk ba a aiwatar ba."

Fusataccen mutumin na nufin lalataccen titin yankin da kuma aikin asibitin Birnin Kudu wanda ya fi shekaru 10 ana aikinsa.

'Ka kasa cika alkawari': fusataccen mutum ya katse gwamna Badaru yana cikin lissafo aiyuka a bainar jama'a
'Ka kasa cika alkawari': fusataccen mutum ya katse gwamna Badaru yana cikin lissafo aiyuka a bainar jama'a
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yadda tsofin gwamnonin jihohin arewa uku suka kirkiri Boko Haram - Musa Dikwa

Babu bata lokaci Badaru ya mayar da martani kamar haka: "Na taba yin alkawarin da ban cika ba? Zan cike alkawarina."

Gwamnan ya ci gaba da danganta laifin rashin cika alkawarin ga 'yan kwangilar da aikin ke hannunsu. Ya danganta su da malalatan gaske.

"Duk da 'yan kwangilar sun karba ne daga gwamnatin da ta gabata, na ci gaba da tabbatar da aikin. Aikin ba ya sauri saboda lalacin 'yan kwangilar," Badaru yayi bayani

"Na biya duk kudin da ake bukata don kammala aikin asibitin. Kudin kwangilarsu bai yi makonni biyu a cikin asusunmu ba. Akwai lokacin da nayi niyyar kwace kwangilar amma kuma lokacin da zai dauka kafin karbar kwangila zai kai lokacin da za ta kammala. Ina tabbatar muku da cewa zan kaddamar da aikin a wannan shekarar," Badaru ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel