An sake kwatawa: Yan bindigan daji sun hallaka dakacin kauye a Zamfara

An sake kwatawa: Yan bindigan daji sun hallaka dakacin kauye a Zamfara

Gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da mummunar hari a cikin karamar hukumar Dansadau na jahar Zamfara, inda suka kashe wasu sarakunan gargajiya biyu muhimmanci kamar yadda rundunar Yansandan jahar ta tabbatar.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito mai magana da yawun rundunar, SP Mohammed Shehu ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 2 ga watan Feburairu inda yace yan bindigan sun kashe Alhaji Gambo Kujemi, dakacin kauyen Kujemi.

KU KARANTA: Almajiranci: Musulmai sun nemi gwamnati ta yi ma iyaye hukunci mai tsauri

Haka zalika, SP Mohammed Shehu ya kara da cewa baya ga kisan dakacin, yan bindigan sun kashe wani mutum daya a yayin da suka kai farmaki a kauyen Karauchi, a karamar hukumar Dansadau, inda a can ne harin ya rutsa da Gambo Kujemi, dakacin Kujemi.

A cewar Shehu yan bindigan sun kai farmakin na da yawansu a kan babura da misalin karfe 8:40 na daren Lahadi, inda suka yi ta harbe harben mai kan uwa da wabi, inda suka kashe har dakacin Karauchi, Mustapha Halilu.

“Bayan samun bayanan hare haren, yansandan Operation Puff Adder tare da Sojoji sun dira kauyen don tabbatar da zaman lafiya da lumana tare da kare sake kai harin yan bindiga a makwabtan kauyukan.

“Muna kira ga jama’a su cigaba da bamu goyon baya tare da bayanan sirri a kan ayyukan miyagun mutane domin mu dauki matakin da ya kamata.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wata mata dattijuwa mai shekaru 70 a duniya, wanda aka sakaya sunanta, ta jagoranci matasa mafarauta zuwa cikin dazuka inda suka kashe yan bindiga 40 a jahar Neja.

Guda daga cikin mafarautan dake cikin tawagar wannan jaruma, Mallam Alhassan ya bayyana cewa ta jagorance su zuwa cikin dajin Zuguruma a karamar hukumar Mashegu na jahar, inda a can suka yi artabu da yan bindiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel