Badakalar layin wayar Hanan Buhari Umarni daga fadar shugaban kasa ne ya sa muka tsare mutumin tsawon makonni ba tare da gurfanar dashi ba – SSS

Badakalar layin wayar Hanan Buhari Umarni daga fadar shugaban kasa ne ya sa muka tsare mutumin tsawon makonni ba tare da gurfanar dashi ba – SSS

Hukumar tsaro ta SSS ta bayyana ma babbar kotun tarayya da ke Asaba a ranar Juma’a cewa ta kama da kuma tsare Anthony Okolie, bisa ga umurnin da ta samu daga fadar Shugaban kasa na bincikar sa kan amfani da layin wayar da Hanan, ‘yar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi amfani dashi a baya.

Okolie dai ya maka hukumar SSS da Hanan a gaban kotu inda ya ke neman abi masa hakkin sa da aka take masa, aka tsare shi har na tsawon makonni 10 ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba a dalilin siyan layin wayar da yayi wanda Hanan Buhari ta taba amfani da shi a chan baya.

Hanan ta bayyana cewa bata umarci rundunar tsaron da su kama kowa ba kan tsohon layin ta da wani ke amfani da shi ba.

Badakalar layin wayar Hanan Buhari Umarni daga fadar shugaban kasa ne ya sa muka tsare mutumin tsawon makonni ba tare da gurfanar dashi ba – SSS
Badakalar layin wayar Hanan Buhari Umarni daga fadar shugaban kasa ne ya sa muka tsare mutumin tsawon makonni ba tare da gurfanar dashi ba – SSS
Asali: UGC

Shi dai Okolie ya sayi layin wayar sa a kamfani, yana cikin harkokin sa sai jami’an SSS suka damke shi wai cewa layin da ‘yar Buhari ce ta taba amfani da shi.

Daga nan aka tisa keyar shi inda aka kulle har na tsawon makonni 10.

Bayan ya fito ne ya kai kara kotu, ya na bukatar a biya shi diyyar tsare shi da aka yi har naira miliyan 500,000,000.

A zaman kotu, Lauyan Hanan ya bayyana cewa babu abun da zai ce game da tattaunawar da ake yi a kotu duk da cewar ya halatta.

Hakan da ya fadi ya fusata Alkalin kotun Nnamdi Dimgba, inda ya ce ta yaya zai ce babu abinda Hanan zata ce game da abun da yake faruwa bayan har da ita aka maka a kotu.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya bada umarnin gina gidaje 10,000 a Borno – Gwamna Zulum

Shi ko lauyan SSS cewa ba samu takardun cikakken bayanin abun da ya faru ba a dalilin ba zai iya cewa komai ba a kai.

Alkalin kotun ya dage shari’ar sai ranar 3 ga watan Maris domin ci gaba da zama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel