Buhari ya bada umarnin gina gidaje 10,000 a Borno – Gwamna Zulum

Buhari ya bada umarnin gina gidaje 10,000 a Borno – Gwamna Zulum

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da gina gidaje 10,000 a jahar Borno domin kara kaimi ga tsarin gwamnatin jahar na sake tsugunar da yan gudun hijira a jahar.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka yayin daya karbi bakuncin tawagar dattawan jahar Borno da Yobe mazauna Abuja da suka kai masa ziyara a Maiduguri ranar Lahadi.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Dan kwallon Najeriya ya kamu da cutar Coronavirus

Zulum ya tabbatar ma tawagar cea shugaban kasa Buhari ya bada umarnin a gina wadannan gidaje domin kara mayar da jahar a yadda take a da cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

“Mun fara manyan ayyukan cigaba a yankuna daban daban tun da dai an dan samu saukin tsaro, saboda ba zamu iya jira har sai an kawo karshen yan ta’adda gaba daya kafin mu fara aiki ba, mun karkatar da hankalinmu daga ayyukan jin kai zuwa cigaban tattalin arziki tare da daidaita jahar.

“Gudunmuwar da gwamnatin tarayya take bamu yana taimaka mana sosai wajen ayyukan jin kai, tare da sake raya jahar. Mun yaba da kulawa ta musamman da shugaban kasa Buhari yake bamu a kokarin samar da zaman lafiya, tsaro da sake gina jahar.

“Ina sanar daku cewa a makon da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a gina gidaje 10,000 a jahar Borno. Amma duk da nasarorin da aka samu a yaki da ta’addanci, har yanzu muna da kalubale wanda shi ne samar ma yan gudun hijira abin yi, ilimin boko da islamiyya, gaskiya mun gaza a wadannan bangarorin.” Inji shi.

A jawabinsa, shugaban tawagar, Ibrahim Bunu ya bayyana cewa sun kafa kungiyar ne don taimakawa a ayyukan jin kai ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, inda yace sun raba kayan abinci da kayan amfani na yau da kullum a jahohin Borno da Yobe.

Sa’annan ya yaba ma gwamnatin jahar, Sojoji, shuwagabannin addinai, da shuwagabannin al’ummai bisa nasarorin da aka samu a yaki da ta’addanci tare da kokarin dawo da zaman lafiya a jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel