Ba na nadamar datse min hannu da shari'a ta yi - Dan jihar Zamfara

Ba na nadamar datse min hannu da shari'a ta yi - Dan jihar Zamfara

A ranar 27 ga watan Janairu na 2000 ne jihar Zamfara ta tabbatar da shari’ar Musulunci bayan kokarin gwamnan na lokacin, Ahmad Sani Yarima, wanda ya fara mulki a 1999.

Daya daga cikin wadanda shari’ar Musuluncin ta ritsa da shi mai suna Lawalli Isa, wanda aka cire wa hannun dama a 2001 a kan satar keke da yayi, ya bayyana matsayarsa a kan yadda lamarin ya shafi rayuwarsa.

A zantawar da jaridar The Punch ta yi da shi, ta tambayesa yadda yake rayuwa bayan an cire masa hannu ta sanadin shari’ar Musulunci a jihar.

Lawalli ya ce, “Ba ni kadai aka cire wa hannu ba a wannan lokacin. Ni ne na biyu a jihar kuma na karshe. Mutum na farko shine Bello Buba Jangebe wanda aka cire wa hannu a 2000 a kan satar Shanu. Ni kuwa an cire min ne a watan Maris na 2001 kuma daga nan ba a karawa wani ba. Na saci keke ne kuma aka cire min hannun dama kamar yadda shari’a ta tanada amma kuma a hakan nake harkokina.”

Bana dana-sani cire min hannu da shari'a ta yi - Dan jihar Zamfara
Bana dana-sani cire min hannu da shari'a ta yi - Dan jihar Zamfara
Asali: UGC

A yayin da aka tambayeshi abinda yake don dogaro da kan shi, ya ce tun bayan da ya warke, ya tuba tare da alkawarin ba zai kara sata ba. Ya kuma shiga siyasa a zamanin tsohuwan jam’iyyar APP har zuwa ANPP da kuma APC.

DUBA WANNAN: Hotunan mutumin kasar Italiya da ya kawo Coronavirus Najeriya

Ya bayyana cewa yana sana’ar noma ne a karamar hukumar Gummi kafin a yanke masa hannun. Yana da karamar gona wacce ba ta iya wadatar da shi har ya shawo kan matsalarsa da ta iyalansa.

A lokacin da aka tambayesa yadda yake ji bayan an cire masa hannu amma ba a ci gaba da shari’ar Musulunci a jihar ba sai yace, “bani da dana-sani gaskiya. Na san abinda aka yi min shari’a ce ta tanadar. Kama ni aka yi kuma aka mika ni gaban kotu. Nasan hakan za ta faru da ni saboda ta faru da wani kuma na gani ai. Kawai haushi na daya ta yadda aka yanke min hannu kuma aka daina shari’ar.”

Lawalli ya bayyana cewa, an kama shi ne da keken sata kuma ya amsa laifinsa a gaban kotun. Bayan amsa laifinsa ne mai shari’ar yace ko ya san hukuncin sata a Musulunci, ya kuma amsa da ya sani. Bayan yanke hukuncin ne aka tambayeshi ko zai daukaka kara amma sai yace ya hakura zai karba hukuncin Allah. A ranar 1 ga watan Maris na 2001 ne aka tsinke masa hannun damansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel