Tirkashi: Na kama mata ta na zina da wani kato a dakin otel - Ahmed Salisu

Tirkashi: Na kama mata ta na zina da wani kato a dakin otel - Ahmed Salisu

- Wani malamin addinin Musulunci mai suna Ahmed Salisu ya koka da yadda ya kama matar shi da wani gardi a otal

- Ya ce tana barazanar kashe shi a duk lokacin da fada ya hada su don ta gaji gidan da ya mallaka

- Matar dai ta musanta kuma ta roki kotun da kada ta raba aurensu don har a lokacin tana kaunar mijinta

Wani malamin addinin Musulunci mai suna Ahmed Salisu ya koka a gaban kotu a kan yadda ya kama matar shi tare da wani kato.

Alkalin kotun, Adeniyi Koledoye, ya ce kotun ba ta da wani dabara daya wuce ta tsinke igiyar aurensu din tunda mai karar ya matsanta a kan saki bayan mutane da yawan da suka saka baki.

“A don haka ne kotun ta tsinke igiyar auren da ke tsakanin Ahmed Salisu da Fatima Salisu. Daga yau dukkanku kun tashi daga ma’auratan juna. Kowannenku zai iya rayuwarshi ba tare da tsangwama ko hantarar juna ba. Kotun na muku fatan alheri.

“Wanda yayi karar zai biya tsohuwar matar tashi N150,000 don ta ci gaba da rayuwarta.” Koledoye y ace.

Mai shari’a Koledoye ya bukaci Salisu da ya dau dawainiyar ci da sha, ilimi da kuma walwalar yaran da suka haifa.

Da farko dai Salisu ya tunkari kotun ne da bukatar ta tsinke auren shi mai shekaru 28 a kan rashin kamun kan matar shi.

“Matata bata da tsoron ubangiji don na kama ta tana lalata da maza da yawa da ke yankinmu. Har karfin halinta ya kai ga tana kawo maza cikin dakinmu. Na taba kama ta dumu-dumu a otal.” Ya ce.

Wanda ke karar ya zargi matar shi din da kokarin kashe shi ta yadda za ta gaji gidan shi.

Mijin ya bayyana cewa matar shi ba ta mutunta dangin shi kuma duk idan suka kai mishi ziyara sai ta ja su da fada.

“Matata bata kaunar ‘yan uwana. Ta taba sarar kanina da wuka wanda har sai da ya kwanta a asibiti. Tana fada da yayata kuma ta sha yi wa kanina ihun barawo idan ya shigo gidana Akwai ranar da aka kusa kona shi amma Ubangiji ya tsare shi.” Ya ce.

Wanda ke karar ya ce kullum matar shi na fitar da wuka tare da barazanar sukar shi in har suka yi fada. Hakan kuwa yasa ya taba guduwa daga gidan shi a 2016.

Ya ce Fatima ta taba fada da shi a titi har ta yaga mishi kayan jikinshi. Ya roki kotun da ta tsinke auren don kuwa ya gaji da shi.

Fatima ta musanta duk zargin da aka yi mata kuma ta roki kotun da kada ta amshi bukatar mijinta don har yanzu tana son shi.

Mahaifiyar yara hudun ta ce babu wata mu’amala da ya taba kama ta tana yi da wani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel