Na shararawa Jonathan karya a lokacin da nake goyon bayan Buhari - Hamma Hayatu

Na shararawa Jonathan karya a lokacin da nake goyon bayan Buhari - Hamma Hayatu

- Hamma Hayatu ya kasance mai goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari amma a yanzu ya jinjinawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

- A wata wallafa da yayi a shafin shi na twitter, wani mai amfani da twitter mai suna Adetutu balogun ya ba Hayatu martani da wancan walafar da yayi a 2015

- Kafin zaben 2015, ma’abota amfani da twitter na Arewa sun karyata cewa Goodluck ya gina sama da makarantun almajirai 100

Hamma Hayatu ya kasance mai goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari amma a yanzu ya jinjinawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a kan gina makaratun almajirai da kuma jami’o’i a Arewa.

A baya dai Hayatu ya karyata aiyukan a lokacin da yake goyon bayan Buhari.

A wata wallafa da yayi a shafin shi na twitter, wani mai amfani da twitter mai suna Adetutu balogun ya ba Hayatu martani da wancan wallafar da yayi a 2015 inda ya karyata aiyukan Jonathan din.

Kafin zaben 2015, ma’abota amfani da twitter na Arewa sun karyata cewa Goodluck ya gina sama da makarantun almajirai 100. Sun san da makarantun amma suka karyata lamarin.

“Kafin zaben 2015, Arewa twitter sun yada karya kan cewa Goodluck bai gina makarantun alamajirai ba. A halin yanzu Buhari ya basu kunya kuma sun sauya salonsu. Sun san da makarantun kafin zaben amma suka ki fadi,” Adetutu yace.

KU KARANTA: Baturen da ya kawo cutar Coronavirus yayi kokarin guduwa daga inda ake tsare shi a Legas

A ranar 10 ga watan Maris 2015, Hayatu ya rubuta: “Yanzu na gama kallon wata karya a Liberty TV na cewa Jonathan ya gina makarantun almajirai. Amma wannan duk karya ce da damfara.”

A watan Afirilun 2015, ya kara da bayyana cewa makarantar almajiran daya ce tak a jihar Kaduna. “A duk fadin jihar Kaduna, makarantar almajirai daya ce gwamnatin Jonathan ta gina a kan babbar hanyar Zaria zuwa Kano,” ya wallafa a twitter.

Amma a watan Nuwamba na 2018, hayatu ya sauya magana tare da jinjinawa tsohon shugaban kasar a kan gina makarantun da ya yi.

“Goodluck Jonathan ya gina makarantun Almajirai da yawa a fadin Arewacin Najeriya inda za a ilimantar dasu, ciyarwa da kuma tufatar da su. Malamansu kuwa gwamnatii take biyansu albashi. A cikin adawa irin ta siyasa, an bar wannan babban aikin na tafiya a banza. Buhari matsala ne.” Hayatu ya wallafa a shafin shi na tuwita a ranar 23 ga watan Fabrairun 2020.

“Goodluck ya gina jami’o’i 9 a arewacin Najeriya, ya gina makarantun almajirai 150 a arewa, ya yi titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna. Muna matukar godiya ga Goodluck a kan abinda ya yi wa jama’a,” ya wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel