Bidiyo: An kama wasu yara da suka boye a cikin wani katafaren shago suka ci abinda suke so suka more

Bidiyo: An kama wasu yara da suka boye a cikin wani katafaren shago suka ci abinda suke so suka more

- Bidiyon wasu yara maza biyu ya nuna yadda suka dinga dibar kayan sha a wani babban shago da ke kasar Ghana

- Matasan an hasko ne inda suke dibar kayan sha kala-kala daga kanta sannan suna mayar da su bayan sun shanye abin ciki

- Ana tunanin wannan bidiyon zai zama jan kunne ga masu manyan shagunan ta yadda zasu dinga kiyaye kayan shagonsu

Wani bidyon matasa biyu daga kasar Ghana ya jawo hankulan jama’a ta yadda suka dinga shanye lemuka a wani babban shago ba tare da an gano su ba.

Matasan da har yanzu ba a san ko su waye ba sun bayyana ne a matsayin abokan juna wadanda suka shirya wannan abu tare. Amma kuma wani abokinsu sai ya nade lamarin a bidiyo.

An gan su ne suna shan lemuka kala-kala daga na shagon sannan suka dinga mayar da gororin lemukan kan kantar da aka ajiye su.

A bidiyon, yaran sun nuna tsananin farin cikinsu ta yadda suka aikata abinda suke yi ba tare da an kama su ba kuma cike da nasara. Suna murna baki bude ko kuma baki har kunne.

Ya kamata wannan ya zama babban jan kunne ga masu manyan shaguna a kan su dinga tsare kayansu da kyau ko kuma su dinga saka CCTV a kowanne lungu na shagunansu.

KU KARANTA: Asiri ya tonu: An kama tsohon sojan sama yana shugabantar wasu takadiran 'yan fashi

Ganin kwastoma ya zo siyan lemu amma sai ya dauko a gano cewa babu komai a cikin gorar zai zama abin zargi ga masu tsaron shagunan.

A wani rahoto na daban, an ji cewa wata mata a birnin Hong Kong da ke kasar China ta kai karenta asibiti amma an gano cewa yana dauke da cutar Coronavirus.

A don haka ne ake shawartar masu dabbobi da su dinga kiyayewa tare da wanke hannunsu a duk lokacin da suka taba dabbobinsu na gida, gudun kamuwa da mugunyar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel