A karon farko an samu wani kare da cutar Coronavirus a birnin Hong Kong

A karon farko an samu wani kare da cutar Coronavirus a birnin Hong Kong

- A kasar China ne a cikin birnin Hong Kong aka gano wani kare dauke da cutar coronavirus

- Kamar yadda mai Karen ta bayyana, babu wata alamar cutar da Karen ya bayyana da ke nuna ba shi da lafiya

- A halin yanzu ana shawartar masu ajiye dabbobi a gida da su dinga wanke hannayensu bayan sun kammala taba dabbobinsu

An gano wani Karen da ke dauke da cutar coronavirus a garin Hong Kong da ke kasar China.

Yvonne Chow Hau Yee ta kai karenta asibitin dabbobi da ke yankin Happy Valley kuma a sakamakon da ya bayyana, an gano cewa Karen na dauke da cutar duk da bai nuna wani alamu na cutar ba.

A karon farko an samu wani kare da cutar Coronavirus a birnin Hong Kong
A karon farko an samu wani kare da cutar Coronavirus a birnin Hong Kong
Asali: Facebook

A halin yanzu dai an ware Karen don karbar magani bayan an gwada shi an gano yana dauke da mugunyar cutar. Jami’ai a bangaren noma da kiwo da kiwon kifi sun bukaci a ware Karen don a ci gaba da duba yadda Karen ke samun karfi.

Amma kuma AFCD a wata takarda da ta fitar ta ce “babu wata shaida da ke nuna cewa dabbobi za su iya kamuwa da cutar ko kuma za zu iya shafawa jama’ar da ke tare da su.”

KU KARANTA: Manyan mabarata 10 na duniya da arzikinsu yafi na wasu manyan masu kudin Najeriya

Ana tunatar da ma’abota ajiye dabbobi da su dinga wanke hannayensu bayan sun tabasu.

Lamarin ya zama na farko da aka samu cutar coronavirus a tare da dabbar cikin gida.

Idan zamu tuna, a ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa an samu mutum daya dauke da muguwar cutar coronavirus wacce ta ke ta halaka jama’a a fadin duniya.

Cutar ta fara ne daga garin Wuhan da ke cikin kasar China. Har a halin yanzu dai ba a gano maganin cutar ba duk da masana kimiyya na ta kokarin ganowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel