Tubabbun 'yan Boko Haram za su mori karatu a kasashen ketare - Majalisa

Tubabbun 'yan Boko Haram za su mori karatu a kasashen ketare - Majalisa

Bukatar kafa cibiyar kula da gyaran tubabban ‘yan Boko Haram za ta samu kudin ayyukanta ne daga hukumar ilimin farko (UBEC) da kuma gidauniyar kudi ta ilimin manyan makarantu (TETFUND), The Punch ta ruwaito.

Sauran hanyoyin samun kudin cibiyar za su hada da tallafi, bashi da kuma gudumawa da ga gwamnatocin jihohi shida na Arewa maso gabas. Jihohin sun hada da Borno, Bauchi, Yobe, Adamawa, Taraba da Gombe.

Bayanin na kunshe a wata takarda da jaridar The Punch ta samu a ranar Alhamis.

Bukatar wacce aka bayyana da samar da cibiyar kasa ta kula da ilimi da gyaran tubabbun ‘yan Boko Haram a Najeriya, ta samu karatun farko a majalisar dattijai a ranar Alhamis din makon da ya gabata.

Bayan sa’o’i kalilan da aka karanta bukatar wacce dan majalisar dattijan mai wakiltar jihar Yobe ta yamma, Ibrahim Geidam ya mika, fusatattun ‘yan Najeriya sun yi martani mai zafi a kan hakan.

Hakazalika, kungiyar gwagwarmaya ta BringBackOurGirls wacce ta dinga assasa zancen ceto ‘yan matan da aka sace a Chibok a 2014, ta ce wannan shirin ya kamata a yi shi ne tare da na gyara dubban jama’ar da suka rasa gidajensu a yankin.

Tubabbun 'yan Boko Haram za su mori karatu a kasashen ketare - Majalisa
Tubabbun 'yan Boko Haram za su mori karatu a kasashen ketare - Majalisa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Mata yanzu suna tafasa audugar mata suna shan ruwan don maye - NDLEA

Amma a ranar Litinin, Geidam ya kare wannan bukatar a zantawa da yayi da manema labarai. Ya ce da yawa ‘yan ta’addan na son ajiye makamansu tare da mika kansu amma suna tsoron abinda za su fuskanta.

Sanatan ya bayyana cewa wannan bukatar ba tana nuna cewa za a kula da ‘yan ta’addan da hukumomin tsaro suka kama bane. Duk wadanda jami’an tsaro suka damke za su fuskanci fushin hukuma.

Ba a kai kwanaki biyu ba da Sanatan ya kare wannan bukatar a gaban majalisar, mayakan Boko Haram 25 tare da matansu suka mika makamai ga rundunar sojin jamhuriyar Nijar kuma aka dawo dasu Borno, jihar Maiduguri a ranar Laraba.

Takardar wannan bukatar kafa cibiyar tubabbun Boko Haram din wacce jaridar The Punch ta gani, ta ce kashi daya na kudin TETFUND da UBEC ne za a yi amfani dasu wajen kafa cibiyar.

Hakazalika cibiyar za ta samu kashi 0.5 na kudin da gwamnatin tarayya ke ba jihohi shida na yankin Arewa maso gabas din.

Bukatar idan ta tabbata, za ta ba tubabbun 'yan ta'addan damar zuwa kasashen ketare karatu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel