Wata sabuwa: Mata yanzu suna tafasa audugar mata suna shan ruwan don maye - NDLEA

Wata sabuwa: Mata yanzu suna tafasa audugar mata suna shan ruwan don maye - NDLEA

- Hukumar hana yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Gombe ta gargadi al'umma kan wata mummunar dabi'a da mata suka kirkiro

- Hukumar ta NDLEA ta ce an gano cewa wasu matan suna tafasa audugar al'ada ta mata da aka yi amfani da shi su sha ruwan domin maye

- Hukumar ta gargadi al'umma cewa wannan dabi'a na da matukar hadari kuma tana iya jefa rayuwar mutane cikin matsala

Hukumar kula da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) reshen jihar Gombe ta ce mata a jihar sun kirkiro da wata sabuwar hanyar yin maye.

A wani taron wayar da kan jama'a a jihar, kwamandan da ke kula da yankin Funakaye na hukumar, Muhammad Alkali, ya ce matakin shaye shayen miyagun kwayoyi a tsakanin mata a Gombe ya karu ne daga jaraba ta al'ada zuwa kwayoyi zuwaga yanzu shan tacaccen ruwan tafasasshen audugar al'ada ta mata domin maye.

Wata sabuwa: Mata sun koma tafasa audugar mata da aka yi amfani da shi suna shan ruwan don maye - NDLEA
Wata sabuwa: Mata sun koma tafasa audugar mata da aka yi amfani da shi suna shan ruwan don maye - NDLEA
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hargitsi tsakanin shugabannin Boko Haram da ISWAP: Akwai yuwuwar Shekau ya sheka lahira

Da yake jawabi a fadar Sarkin Funakaye inda aka gudanar da taron wayar dakai din, Alkali ya ce

“An jawo hankalin mu zuwa ga cewa galibin masu shan kwayoyin sun yi wata dabara ta yin maye ba tare da shan abubuwan da doka ta hana ba ko kuma sanannun kwayoyin maye. A yanzu suna tafasa audigar tsafta ta mata hade da wasu abubuwan, galibi shara, suna tace ruwa kafin a sha

"Kun ga wannan mummunan abu ne a ga mutane, hakika al'ummarmu tana matukar bukatar taimakon dukkan masu fada a ji a cikin wannan gwagwarmaya tunda NDLEA ba zata iya ita kadai ba".

A wani rahoton, kun ji cewa a kalla mutane 13 ne suka rasu sakamakon hatsarin mota da suka faru a jihar Bauchi a daren ranar Alhamis da safiyar ranar Juma'a.

The Punch ta ruwaito cewa hatsarin motocin sun faru ne a Tashan Maiturare da Takandan Giwa duk a babban titin Bauchi zuwa Jos a karamar hukumar Toro a jihar ta Bauchi.

A hatsarin na farko wadda ya faru misalin karfe 9 na daren ranar Alhamis, a kalla mutane 11 ne suka mutu nan take yayin da wasu da dama suka jikkata.

Hatsarin na biyu ya faru ne a subahin ranar Juma'a kusa da kauyen Takandan Giwa yayinda wata mota ta kauce daga titi ta fada cikin daji inda mutane biyu suka mutu yayin da wasu kuma suka samu rauni.

Da aka tuntube shi, Shugaban sashin ayyuka na hukumar kiyaye haddura na kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi, Ibrahim Abubakar ya tabbatar da afkuwar hadduran amma ya ce har yanzu suna tattara bayanai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel