Hukumar WHO ta duniya ta yaba da kokarin Najeriya na yaki da cutar Coronavirus

Hukumar WHO ta duniya ta yaba da kokarin Najeriya na yaki da cutar Coronavirus

Babban jami’in hukumar lafiya ta duniya, ta majalisar dinkin duniya, WHO, a Najeriya, Dakta Clement Peter ya jinjina ma namijin kokarin da Najeriya take yi wajen yaki da cutar Coronavirus tun bayan bullarta a Najeriya.

Peter ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja, a cikin ma’aikatar kiwon lafiya, inda yace abin a yaba ne yadda Najeriya ta yi gaggawar gano cutar a Legas, kuma tana kula da shi.

KU KARANTA: Jerin bayanai 11 da ba su inganta ba dangane da cutar Coronavirus

Hukumar WHO ta duniya ta yaba da kokarin Najeriya na yaki da cutar Coronavirus
Hukumar WHO ta duniya ta yaba da kokarin Najeriya na yaki da cutar Coronavirus
Asali: UGC

“Muna aiki tare da hukumar takaita wanzuwar cututtuka ta Najeriya, NCDC, don bayar da gudunmuwa a kan yadda za’a takaita wanzuwar cutar, ina alfahari da cewa NCDC ta ciri tuta daga cikin takwarorinta a nahiyar Afirka gaba daya.

“Kuma zamu cigaba da aiki kafada da kafada da ita don shawo kan matsalar, a yanzu da muka samu rahoton matsalar a Najeriya, abin da ya fi kamata shi ne takaita wanzuwar ta, kuma zamu janyo sauran masu ruwa da tsaki don baiwa Najeriya gudunmuwa.” Inji shi.

Sai dai Clement ya yi kira ga yan jaridu su dinga bayar da ingantattun bayanan da suka dace dangane da Coronavirus, kuma su sanar da jama’a a kan muhimman abubuwan da ya kamata su yi don kare kansu daga kamuwa da cutar.

Da yake jawabin yadda cutar ta shigo Najeriya, Ministan kiwon lafiya, Dakta Osagie Enahire yace mutumin da aka samu cutar a jikinsa dan kasar Italiya ne, kuma ya yi tafiya zuwa kasarsu ne, inda ya dawo a ranar 20 ga watan Feburairu.

“A ranar daya dawo lafiyarsa kalau, washe gari ne ya fara rashin lafiya, daga nan ya wuce asibiti inda likita ya duba shi, an yi masa gwajin zazzabin cizon sauro amma ba samu a jikinsa ba, nan da nan aka tura shi dakin gwaje gwaje na asibitin koyarwa na jami’ar Legas, a can aka gano cutar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel