PDP ta dorawa Buhari laifin shigowar Coronavirus Nigeria

PDP ta dorawa Buhari laifin shigowar Coronavirus Nigeria

Jam’iyyar ada wata Peoples Democratic Party PDP, ta dorawa shugaban kasa Muhammadu Buhari laifin shigowar cutar Coronavirus cikin Nigeria.

Jaridar Legit Hausa ta rahoto yadda gwamnatin Nigeria da safiyar Juma’a ta tabbatar da bullowar cutar coronavirus ta farko a kasar.An gano cutar ne a jikin wani dan kasar Italiya daya shigo cikin kasar.

Bullowar ta Nigeria itace ta farko a fadin Nahiyar Africa data kashe miliyoyin mutane a fadin duniya, mafi yawa a kasar Sin inda asalin cutar ta faro.

Mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Kola Ologbdiyan, a wani jawabi ya bayyana cewa “A bayyana yake cewa gwamnatin Buhari bata gudanar da aikinta yadda ya kamata ba, bata dau wani kwakkwaran mataki ba akan cutar, har ya kawo izuwa hali na tsoro da ake ciki yanzu”

Kola Ologbodiyan ya ce gwamnatin Buhari bata dau wani mataki ba na taimakawa yan Nigeria da ke kasar Sin ba duk da rokon da sukayi akan hakan, tamkar yadda suka bar wadanda aka kashe a harin kin jinin bakin fata a kasar Afrika ta kudu.

Ya kara da cewa yan Nigeria su kama gwamnatin Buhari da laifi idan har masifar Coronavirus ta watsu tare da matsalar tattalin arziki da rashin tsaro da muke fama da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel