Coronavirus: Najeriya ta na da isassun kayan aikin gano cutar - Gwamnatin tarayya

Coronavirus: Najeriya ta na da isassun kayan aikin gano cutar - Gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da tabbacin cewa tana da isassun kayayyakin ganowa da kuma yakar cutar Coronavirus

- Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai kan tanadin gwamnati game da lamarin

- Ya roki yan Najeriya da kada su tayar da hankalinsu

Gwamnatin tarayya ta ba yan Najeriya tabbacin cewa tana da isassun kayayyakin ganowa da kuma yakar cutar Coronavirus.

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai kan matakin gwamnatin tarayya kan cutar Coronavirus, biyo bayan tabbatar da samun lamarin a Najeriya.

Coronavirus: Najeriya ta na da isassun kayan aikin gano cutar - Gwamnatin tarayya
Coronavirus: Najeriya ta na da isassun kayan aikin gano cutar - Gwamnatin tarayya
Asali: UGC

Ya roki yan Najeriya da kada su tayar da hankalinsu, cewa “Mun san cewa a irin wannan lokacin, za a ta yada labaran karya da jita-jita. Don haka muna bukatar yan Najeriya da kada su fada a tarkon masu watsa labaran karya”.

“A yanzu haka Facebook na aiki tare da mu kan wannan lamari. Sun bukaci yan Najeriya da su kai rahoton labaran karya ko mai batarwa kan shafukan Facebook da Instagram don ayi gaggawan sauke su.

“Sun kuma bamu tabbacin cewa suna daukar mataki don cire duk wani sako na karya ko wanda ka iya zama hatsari game da wannan lamari da kiwon lafiyar jama’a a Najeriya,” in ji shi.

Alhaji Lai ya kuma bayyana cewa an umurci ma’aikatar labarai da al’adu irin su NTA, FRCN, NAN, VON da NOA da su jajirce a kokarinsu na wayar da kan yan Najeriya da bayanan da ya kamata don zama lafiya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dan Italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus ya ziyarci Ogun

A wani labarin kuma mun ji cewa, Lafarge Africa Plc, wata kamfanin siminti ta tabbatar da cewar dan kasar Italiyan da ya kasance mutum na farko da aka samu yana dauke da cutar Coronavirus a Najeriya ya ziyarce ta a Ekwekoro, jahar Ogun.

Folashade Ambrose-Medebem, kakakin kamfanin, ta bayyana hakan a wani jawabi a ranar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu.

Ta ce an gano dukkanin wadanda suka yi hulda da dan kasar Italiyan wanda ba a bayyana kowanene ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel