Labarin Ramatu matar da take samun ribar miliyan daya da rabi a kowanne mako da sana'ar sayar da carbin malam

Labarin Ramatu matar da take samun ribar miliyan daya da rabi a kowanne mako da sana'ar sayar da carbin malam

- Ramatu wata mata ce ‘yar asalin jihar Katsina da ke da babban kamfanin da ta dauka ma’aikata 70

- Kamfanin nata dai na hada wata alawar yara ce wacce ake kira da charbin mallam

- Ramatu ta bayyana yadda ta rabu da mijinta sannan ta siyar da kadarorinta tare da kafa sana’ar da ke samar mata da miliyoyi a mako daya

Ramatu wacce aka fi sani da bebi mata ce mai zama a kauyen Fadima da ke jihar Katsina a Najeriya. Tana da ma’aikata sama da 70 sakamakon babban kamfani da ta mallaka a kauyensu. Tana yi alawar yara wanda aka fi sani da Charbin Mallam.

A wata tattaunawa da tayi da gidan talabijin din Cliqq TV, Ramatu ta bayyana cewa ta siyar da duk kadarorinta ne bayan aurenta ya mutu. Ramatu ta bayyana yadda mahaifiyarta da dan uwanta suka hana ta bashin kudi don fara kasuwanci.

“Kanwar mahaifiyata ta koya min yadda zan dinga yin charbin Mallam din. Bayan mutuwar aurena, na yanke shawarar koyon sana’a, wanda kuma na samu kanwar mahaifiyata ta koya min. Na roki mahaifiyata da kanina a kan su ara min kudi in fara amma sai dukkansu suka hana ni. Daga nan sai na siyar da kadarorina sannan na hada babban jari na fara wannan kasuwancin.” Ramatu ta sanar da Cliqq TV.

KU KARANTA: Tirkashi: Matar aure ta gano takardar dake nuni da cewa ta mutu a cikin motar mijinta

A yau, Ramatu na samun kudi daga kasuwanciinta fiye da wanda kanwar mahaifiyarta da ta koya mata take samu.

Charbin Mallam dai alawa ne wanda ake hadawa a gida amma an fi yin shi a kasar Hausa. Ana yin shi da sikari ne tare da kwakwa sai a kulla shi tamkar charbi a farar leda.

“Ina amfani da sikari buhu 10 zuwa 13 a kowacce rana kuma ina siyar da na dubu dari biyu a kowacce rana” Ramatu ta kara da cewa.

Tana siyar da wannan suwit din a fadin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina. Ramatu ta kara da kira ga gwamnati da ta taimaka wajen saka hannun jari a irin sana’o’insu don karfafa su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel