Tirkashi: Matar aure ta gano takardar dake nuni da cewa ta mutu a cikin motar mijinta

Tirkashi: Matar aure ta gano takardar dake nuni da cewa ta mutu a cikin motar mijinta

- Wata ma’aikaciyar jinya mai yara hudu a jihar Legas ta yi bayanin yadda ta samu takardar shaidar mutuwarta a motar mijinta

- Ta bayyana cewa ta taba gano cewa yana soyayya da wata mata mai kusan shekaru 40

- Amma kawai wata rana sai ta tarar da fasfotin shi da Visa tare da na matar don zasu tsallaka Amurka tare da shaidar mutuwarta

Wata ma’aikaciyar jinya a jihar Legas mai ‘ya’ya hudu ta yi bayanin yadda ta samu takardar shaidar mutuwarta a motar mijinta, uban ‘ya’yanta.

Ta bayyana wannan labarin ne ga Toke Makinwa wanda ya wallafa a shafinshi na tuwita.

Kamar yadda ya wallafa: “Ina cikin matukar bakin ciki da kunar zuciya. Bacin rai da takaici duk sun cika ni. Ina da aure kuma yarana hudu. A tunanina mijina ya fi na kowa a duniya.

“Ni kwararriyar ma’aikaciyar jinya ce a wani asibitin gwamnati da ke jihar Legas. Shi kuwa mijina likitan hakori ne. Muna ta shirin komawa Amurka idan dan mu na farko ya kammala karatun firamare.

“Kusan shekara daya da ta gabata ne mijina ya fara soyayya da wata mata da ta kusa shekaru 40. Na ga sakonninta kuma da na tambaya mijina sai ya bani hakuri tare da neman yafiyata.

“Amma kuma wani abin mamaki sai mijina bai dawo gida a ranar Juma’a ba. Ranar Asabar kuwa sai ya dawo. Bayan na dau motar shi don in je ciko gas din girki, sai na ga wani ambulan wanda na bude.

“A cikin ambulan din na ga fasfotinsa tare da Visa ta shiga Amurka da ta wannan budurwar da ya fara soyayya da ita. Na ga wani fom da yayi amfani da shi wajen cike Visa din. A wannan fom din ne na ga ya saka matar shi ta mutu kuma ya hada da takardar shaidar mutuwata tare da shaidar auren shi da budurwar.

“A wannan fom din ya rubuta sunayen yaranmu amma yayi ikirarin cewa na mutu. Na rasa yadda zanyi. Yana ta tambayata me ya faru bayan na isa gida. Me zanyi mishi don in huce takaicin nan?”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel