Matar da ta rubuta jarrabawa awanni kadan bayan ta haihu ta fita da sakamako mai kyau

Matar da ta rubuta jarrabawa awanni kadan bayan ta haihu ta fita da sakamako mai kyau

- Wata mahaifiya mai karancin shekaru ta jawo hankulan jama’a ta yadda ta nuna kwazonta a fili

- Ta yi jarabawa jim kadan bayan ta haihu kuma ta samu gagaruwamar nasara a jarabawar

- Mai jegon ta ce, duk da malamanta sun shawarceta da kada ta rubuta jarabawar don ba za ta ci ba, ta jajirce kuma ta rubuta

Wata mahaifiya mai kananan shekaru ta jawo hankulan mutane a kafafen sada zumunta sakamakon kwazon da ta nuna yayin jarabawar da ta yi bayan lokaci kalilan da ta haihu.

Duk da mutane da yawa wadanda suka hada da malamanta sun bayyana cewa ba dole ta ci jarabawar ba, Kiara Nelson ta karyata hasashen nasu.

Matar da ta rubuta jarrabawa awanni kadan bayan ta haihu ta fita da sakamako mai kyau
Matar da ta rubuta jarrabawa awanni kadan bayan ta haihu ta fita da sakamako mai kyau
Asali: Facebook

Labarinta ya ba mutane da yawa mamaki sannan sun dinga jinjina mata yadda ta jajirce duk da rashin kwarin guiwar da ta dinga samu.

Kiara ta wallafa hotunanta a yayin da take gadon asibiti bayan ta haihu. Ta bayyana cewa akwai jarabawar da za ta yi ta nan ba da dadewa ba bayan ta haihun.

KU KARANTA: Wannan rashin imani dame yayi kama: 'Yan bindiga sun yiwa budurwa fyade sannan suka kashe mahaifinta akan idon ta

Tana da ciwon tsinkau-tsinkau wanda yasa ta haihu bayan makonni 35 da daukar cikin, wanda yayi wuri da yadda aka yi tunanin za ta haihu.

Laulayin cikin tare da karatun jarabawar yasa malamanta suka bata shawarar hakura da jarabawar saboda ba dole ta iya rubutawa ba bayan ta haihu.

“Na yi nasarar jarabawar duk da an ce in ajiye ba dole in ci ba,” ta rubuta a shafinta na Facebook.

“Duk da na haifa yarinya mace kuma ina fama da aiyukan makaranta, ba zan hakura ba. Zan iya ci gaba da aiyukan makaranta na koda kuwa shayarwa nake yi.” Kiara ta ce.

Mahaifiyar mai kwarin guiwa ta ce ba ta dana sanin daukar wannan matakin duk da akwai hatsari a ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng