Budurwa ta makance bayan ta je anyi mata fenti a cikin kwayar ido ya koma baki

Budurwa ta makance bayan ta je anyi mata fenti a cikin kwayar ido ya koma baki

- Wata budurwa ta fada mawuyacin hali bayan da ta je a rina mata kwayar idonta ya koma baki

- Aleksandra Sadowska budurwa ce mai shekaru 25 wacce mai rina ido ya kashe mata kwayar ido

- An yanke mishi hukuncin shekaru uku a gidan yari sakamakon rashin sanin makamar aikinsa da kuma ganganci

Garin neman kiba ne wata budurwa ta jawo wa kanta rama. Wajen kwaliya da son a birge ne ta mayar da kanta makauniya. Ta kai kanta ne wajen masu rina kwayar ido amma sai aka yi rashin sa’a ta zama makauniya.

Aleksandra Sadowska ‘yar asalin birnin Wroclaw ce a yammacin Poland. Tana da shekaru 25 kuma a wajen rina kwayar idonta ne ta zama makauniya. Ta so yin koyi da mawakin gambarar nan mai suna Popek ne wanda ya rina kwayar idon shi zuwa baki.

Budurwa ta makance bayan ta je anyi mata fenti a cikin kwayar ido ya koma baki
Budurwa ta makance bayan ta je anyi mata fenti a cikin kwayar ido ya koma baki
Asali: Facebook

Bayan an gama bin duk wasu hanyoyin da suka dace don mayar da kwayar idon baki, Aleksandra ta fara korafin ciwon ido amma sai mai rina idon ya ce mata kada ta damu. Ya shawarceta da ta sha maganin kashe zafi.

Amma kuma bayan ta daina gani kwata-kwata, likitoci sun sanar da budurwar cewa ba za ta taba warkewa ba kuma idonta na hagu zai daina gani nan ba da dadewa ba.

KU KARANTA: Sani Danja ya bude katon kamfanin sayar da motoci a birnin Abuja

Tuni dai aka damke wanda yayi mata aiki a idon mai suna Piotr A, kuma zai kwashe shekaru uku a gidan yari sakamakon makantar da ita da yayi ba da gangan ba.

A yayin da aka ci gaba da bincike, an gano cewa wanda yayi mata aikin idon yyai kura-kurai masu tarin yawa a yayin yi mata aikin. Ya yi amfani da ruwan rinin da ake yi wa jiki wanda kuma ba a so ya taba ido kwata-kwata.

Lauyan budurwar ya sanar da kafafen yada labarai cewa: “A bayyane yake idan aka ce mai aikin idon bai san yadda ake yi ba. Haka kuma ya dage wajen jefa rayuwar budurwar cikin mugun hali.”

Aleksandra ta ce: “Wannan abu bai yi dadi ba. A halin yanzu dai likitoci ba su bani karfin guiwar jin sauki ba. Ya yi min illa babba. Ina tsoron zan makance duka. Ba zan rufe kaina a gida in ci gaba da fama da bacin rai ba. Dole ne in fito in ci gaba da rayuwa.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel