Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da wanda ya kawo Coronavirus Najeriya

Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da wanda ya kawo Coronavirus Najeriya

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya tabbatar da bullar cutar Coronavirus mai kisa a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma'ar nan 28 ga watan Fabrairu.

A yadda sanarwar ta nuna, cutar ta shafi wani dan kasar Italiya ne wanda yake aiki a Najeriya, wanda ya dawo daga birnin Milan ya shigo Legas a ranar 25 ga watan Fabrairu.

An tabbatar da cutar a jikinshi, bayan gabatar da gwaje-gwaje a babban asibitin koyarwa na jami'ar Legas, a fannin binciken cututtuka.

Ma'aikatar lafiyan ta tabbatar da cewa, mutumin yana nan yana karbar magani, kuma yana samun sauki a hankali a hankali.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin Najeriya karkashin ma'aikatar lafiya na iya bakin kokarinta wajen daukar mataki akan yaduwar cutar.

"Muna so mu tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa mun cigaba da daura damarar yaki da wannan cuta tun lokacin da muka samu labarin bullurta a kasar China, kuma zamu yi amfani da duk wata hanya da gwamnati za ta bayar wajen ganin mun hana cutar yaduwa."

KU KARANTA: Mun bazama neman duk wadanda ya hadu da su lokacin da ya shigo Najeriya - Gwamnatin Legas kan wanda ya shigo da Coronavirus

Ga abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da mutumin da ya shigo da cutar Najeriya:

1. Dan asalin kasar Italiya ne

2. A Najeriya yake aiki amma ya je gida inda ya debo ta kuma kawo mana nan

3. Ya dawo Najeriya tun ranar Talata, 25 ga Febrairu, 2020

4. Yana boye yanzu kuma babu alamun rashin lafiya tattare da shi

5. Kwana daya bayan dawowa ya fara nuna alamun rashin lafiya inda aka kaishi asibiti

6. An bazama neman wadanda ya hadu da su tun ranar da ya shigo

Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da wanda ya kawo Coronavirus Najeriya
Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da wanda ya kawo Coronavirus Najeriya
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel