Za’a tura tubabbun mayakan Boko Haram jami’o’in kasashen waje don yin karatu

Za’a tura tubabbun mayakan Boko Haram jami’o’in kasashen waje don yin karatu

Wata kudurin doka dake gaban Sanatocin Najeriya a majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta dauki nauyin karatun tubabbun mayakan Boko Haram zuwa manyan jami’o’in kasashen waje domin su karo ilimi.

Jaridar Punch ta ruwaito kudurin ya bukaci a kafa sabuwar hukumar da za ta kula da tubabbun yan Boko Haram, kuma ta bukaci hukumar ilimi ta bai daya, UBEC, tare da hukumar kula da ilimin gaba da sakandari ta Najeriya su samar da kudaden tafiyar da hukumar.

KU KARANTA: Gwamnatin Amurka ta baiwa Masallatai daman kirar Sallah ta lasifika

Haka zalika kudurin dokar ta nemi gwamnatocin jahohin Arewa maso gabas da suka hada da Borno, Bauchi, Yobe, Taraba, Adamawa da Gombe za su dinga baiwa hukumar kudaden gudanarwa, sai kuma kudaden tallafi da ake sa ran hukumar za ta samu.

Tsohon gwamnan jahar Yobe, wanda a yanzu yake wakiltar al’ummar mazabar Yobe ta gabas a majalisar dattawa, Sanata Ibrahim Gaidam ne ya gabatar da wannan kuduri a majalisar, kuma a ranar Alhamis din makon da ta gabata ne kudurin ya tsallake karatu na farko.

Sai dai yan Najeriya da dama sun nuna bacin ransu game da samar da wannan kudurin doka, inda suka yi kira ga yan majalisu da su yi fatali da kudurin tare da duk abubuwan da ya kunsa a cikinsa.

Amma Sanata Gaidam yak are kudurin, inda yace akwai yan Boko Haram da dama dake kokarin ajiye makamansu, kuma su mika wuya, amma suna tsoron abin da zai iya biyo baya, ya kara da cewa babu ruwan dokar da duk wani dan Boko Haram da Sojoji suka kama, domin wadannan zasu fuskanci fushin doka ne.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jahar Kano ta kammala shirin daukan sabbin jami’an tsaro guda 2,200 domin taimaka ma hukumomin tsaro dake jahar wajen samar da ingantaccen tsaro.

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Abba Anwar a ranar Alhamis, wanda ya bayyana cewa za’a dauki matasan ne daga kananan hukumomin jahar 44, inda kowacce karamar hukumar za ta samu jami’ai 50.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel