Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci

Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci

- Wata baturiya 'yar asalin kasar Scotland ta debo yaranta guda biyu ba ta zame ko ina ba sai kasar Uganda domin ta ba su misali

- Baturiyar ta yi hakane domin ta basu misali da ainahin abinda ake kira da talauci, bayan sun dame ta da korafin akan cewa danginsu talakawa ne

- Matar mai suna Ziz ta bayyana cewa 'ya'yan nata Nia da Robyn sun ga abubuwan da basu taba gani ba, inda suka ga yara cikin tsumma da kafafunsu babu takalmi, sannan makarantu babu abubuwan rubutu dana karatu

Awani rahoto da The Sun ta fitar ranar 23 ga watan Fabrairu, 2020, wata mata mai suna Ziz daga kasar Scotland, ta gaji da korafin da ‘ya’yanta guda biyu suke yi mata, Nia mai shekaru 9 sai kuma Robyn mai shekaru 8, inda ko da yaushe suke yi mata korafin cewa danginsu talakawa ne.

Wannan daliline ya sanya Ziz ta dauko su takanas daga kasarsu basu dire a ko ina ba sai kasar Uganda, inda ta bayyana cewa tayi hakane domin ta nunawa ‘ya’yan nata ainahin abinda ake kira da talauci.

Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci
Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci
Asali: Facebook

“Kafin mu zo Uganda, ‘ya’yana suna ta faman yi mini korafi akan cewa mu talakawa ne, saboda suna ganin abokanansu suna zuwa wuraren shakatawa a lokacin hutu,” ta ce na ce musu, “kuna da wajen kwana, baku da matsalar kudi, muna siyan duk abinda muke so, muna da ikon zuwa duk inda muke so, kuma muna zaune a cikin kasar da take jerin kasashe 5 mafi arziki a duniya.”

KU KARANTA: Tashin hankali: An kama ta saka saurayinta a cikin jaka ta datse da mukulli har sai da ya mutu

Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci
Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci
Asali: Facebook

Wadannan yara dai basu yadda da abinda mahaifiyar ta su take fada musu ba, inda suke ce mata basu da babban gida da masu aiki, hakan ya sanya Ziz ta yanke hukuncin nuna musu yadda mutanen kasar Uganda suke rayuwa.

“Muna zaune cikin jin dadi koda yaushe, na tabbata abinda suka gani a Uganda ya koya musu darasi,” ta ce “ina jin abinda yafi daga musu hankali shine yadda suka gansu ko kayan sawa basu da shi, sunga da yawa daga cikin mutanen yankin cikin tsummokara. Sun ga cewa mutane na wahala akan abinda mu bamu dauke shi a bakin komai ba. Yara a kasar Uganda basu da abin rubutu da kayan sawa. Da yawa basu da takalmi ko kayan wasa.”

Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci
Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci
Asali: Facebook

Duk da dai cewa Niya da Robin basu taba ganin wani ya mutu saboda zazzabin cizon sauro ko rashin kyakkyawan abinci ba a Uganda, Ziz ta ce, “abinda suka gani a yanzu ya ishe su sanin cewa kasar Uganda tana bukatar taimako. Ina fatan cewa Turawa irina za su yi koyi dani.”

Nahiyar Afrika dai ta zama tushe da dandali na talauci da yunwa da bala'in tashin hankali na rayuwa, hakan ya samo asali da rashin shugabanni nagari da kasashen nahiyar suke fama da shi.

Kasar Scotland dai tana daya daga cikin manyan kasashe guda biyar da suka yi fice a duniya ta fannin tattalin arziki, zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci
Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci
Asali: Facebook

Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci
Baturiya ta kai 'ya'yanta kasar Uganda don su ga ainahin abinda ake kira da talauci
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel