Hargitsi tsakanin shugabannin Boko Haram da ISWAP: Akwai yuwuwar Shekau ya sheka lahira

Hargitsi tsakanin shugabannin Boko Haram da ISWAP: Akwai yuwuwar Shekau ya sheka lahira

An samu hargitsi da tashin hankali a tsakanin manyan Boko Haram da ISWAP, manyan kungiyoyin ‘yan ta’addan da suka hana yankin Arewa maso gabas din kasar nan sakat, wata majiya ta sanar da jaridar The Nation.

Wata majiya mai karfi wacce take makusanciya ga wasu tubabbun kwamandojin Boko Haram din, ta ce akwai shirin da ake yi na halaka shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, sakamakon karuwar rashin yadda da kuma bukatar mulki a kungiyar.

Kamar yadda majiyar ta bayyana kuma ta bukaci da a sakayata, ta ce da yawa daga cikin kwamandojin Boko Haram da ISWAP an kashesu sakamakon yaki da ta’addancin da sojin Najerya suke yi.

An gano cewa sabon rikici ya barke a cikin sansanin ‘yan ta’addan bayan mutuwar Muhammad Shuwa, Abu-Mossad Albarnawee da kuma Baa Idirisa, a ranar 9 ga watan Fabrairun 2020.

Mutuwar manyan kwamandojin ta kawo zargi da rashin yadda da juna a sansanin su Shekau.

Majiyar ta ce, da yawa daga cikin manyan mayaka da kwamandojin Shekau duk sun bar shi kuma a sirrance suke shirin halaka shi.

Ana zaman dar-dar a Boko Haram yayin da Kwamandojin ISWAP suka juya wa Shekau baya
Ana zaman dar-dar a Boko Haram yayin da Kwamandojin ISWAP suka juya wa Shekau baya
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Wani mutum ya sake daka tsalle ya fada ruwa a Legas

Kamar yadda majiyar ta kara da cewa, “Manyan kwamandojin da ke karkashin shugabancin Mallam Bakura suna shirin kashe Shekau saboda rashin bin asalin ka’idojin addini da aka gina Boko haram a kan ta.”

“Sun kara da zargarsa da kashe wasu manyan kwamandojin da yake gani a matsayin kalubale ga shugabancinsa. Hakazalika, an gano cewa Shekau ba ya iya danne sha’awar mata wadanda suka hada da ‘yan kungiyar da kuma yaransu mata.” majiyar ta ce.

Duk wadannan, majiyar tace ya raba shi da manyan kwamandojinsa kuma yasa suke shirin halaka shi. Lokaci kawai suke jira za a rasa Shekau.

Majiyar ta kara da cewa, “Tabbas Shekau zai sheka lahira kuma na zagaye da shi ne za su aika da shi sakamakon yadda yake bibiyar yaransu mata masu kananan shekaru da kuma matansu na aure. Yawan amfani da kananan yara don kunar bakin wake abin dubawa ne.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel