Bayelsa: Lyon ya yi martani a kan hukuncin kotun koli
- David Lyon ya yi martani a kan hukuncin kotun koli wanda ta soke bukatar jam’iyyar APC na sake duba shari’ar zaben jihar
- A ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairu na 2020 ne kotun kolin ta soke bukatar da Lyon tare da jam’iyyar APC suka mika na kara duban shari’ar
- Lyon ya ce ya karba hukuncin saboda zaman lafiya da kuma ci gaban jiharsa ta Bayelsa ne
David Lyon, tubabben gwamnan jihar Bayelsa, ya ce ya karba hukuncin kotun kolin ta yadda ta soke nasararsa a zaben ranar 16 ga watan Nuwamba na 2019.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a wata takarda da ya sa hannu da kansa, ya ce duk da hukuncin kotun kolin na ranar 13 ga watan Fabrairu ya saba ra’ayin jama’ar jihar Bayelsa, ya karba hakan da hannu bibbiyu don zaman lafiya da ci gaban jihar Bayelsa.
Legit.ng ta gano cewa, ya roki magoya bayan jam’iyyar APC da kuma ‘yan jihar Bayelsa wadanda suka fito kwan su da kwarkwatarsu don zabensa, da su karba hukuncin tare da tabbatar da zaman lafiyar jihar.
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An fitar da sakamakon gwajin cutar Coronavirus da aka yi wa wani ɗan China a Legas
Lyon ya jinjinawa shugabannin jam’iyyar APC ta jihar da na kasa a kan yadda suka rungumi damokaradiyya da kuma kundin tsarin mulki.
Ya ce: “Kotun koli a ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairu ta duba shari’ar ranar 13 ga watan Fabrairu amma sai ta ce hukuncinta na farko ne dai-dai."
“Na san yadda wannan hukuncin ya kawo zubewar burin mutanen jihar Bayelsa. A don haka ne nake sanar da ku cewa na rungumi hukuncin kotun kolin komai rashin dadinsa. Hukuncin kotun koli ne kuma dole mu bi shi a matsayin masu bin dokar kasa.” ya kara da cewa.
“Ina so in yi amfani da wannan damar wajen kira ga magoya bayana, jama’ar jihar Bayelsa da kuma masu son zaman lafiya da adalci, da su karba hukuncin don tabbatr da zaman lafiya. A yayin da za su yi tunanin babu adalci a wannan shari’ar, ina kira ga jama’a da su kwantar da hankali tare da gudun kowacce irin tarzoma don ci gaban jihar nan.” in ji shi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng