Damfarar N1.5bn: EFCC ta kama tsohon Kakakin majalisar jihar Kano, Ali-Danja

Damfarar N1.5bn: EFCC ta kama tsohon Kakakin majalisar jihar Kano, Ali-Danja

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC a Kano ta kama tsohon Kakakin mjalisar jihar Kano, Isiyaku Ali-Danja kan zarginsa da yin amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba da kuma bannatar da makuden miliyoyi na aikin mazabarsa.

Mai magana da yawun EFCC, Tony Orilade ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Ya ce an kama Ali-Danja ne bayan an shigar da korafi a kan cewa ya karkatar da wasu makuden kudade da ya kamata gwamnatin Kano ta biya haraji ga hukumar tattara haraji na tarayya (FIRS).

Mista Orilade ya ce an bannatar da kudin da adadinsa ya kai Naira miliyan 1.5 daga asusun ajiyar gwamnatin jihar ta Kano kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Damfarar N1.5bn: EFCC ta kama tsohon Kakakin majalisar jihar Kano
Damfarar N1.5bn: EFCC ta kama tsohon Kakakin majalisar jihar Kano
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kwankwaso ya jahilci yadda kotu ke aikin ta - Kwamishinan Ganduje

An kama Ali-Danja ne kwanaki kadan bayan kama kwamishinan ayyuka na musamman da ake zargi da damfarar kudi Naira miliyan 86.

Sanarwar ta ce, "An gano kudade da dama da aka aike zuwa asusun ajiyar bankunan mutane da dama ciki har da wani kamfani mai suna Allad Drilliing Limited, kamfanin da Ali-Danja ne kadai ke da damar saka hannu kafin a fitar da kudi daga asusun kamfanin."

"Idan ba a manta ba a baya EFCC ta kama kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Kano, Mukhtar Ishaq kan zarginsa da karkatar da kudaden da ya kamata a yi wa karamar hukumar Kano Municipal aiki a lokacin da ya ke shugaban karamar hukumar.

"An kama Mukhtar ne bayan da aka shigar da korafi a kan Mukhtar ga EFCC kan zarginsa da karkatar da kudaden kwangila da ayyukan cigaba da raya mutane a lokacin da ya ke shugaban karamar hukuma."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel