Kwamacala: Mijina mai kanjamau ya auri 'ya ta, sun kuma hada baki sun kore ni daga gidan - Mata ta koka

Kwamacala: Mijina mai kanjamau ya auri 'ya ta, sun kuma hada baki sun kore ni daga gidan - Mata ta koka

- Wata mata mai suna Grace ‘yar asalin kasar Kenya ta bayyana yadda mijinta ya auri diyarta

- Ta ce mijinta ya siyar da filayen shi da duk wasu kadarorin shi inda ya auri yar da ta zo da ita daga wani gida duk da yana dauke da HIV

- Grace ta bayyana cewa, mijinta manemin mata ne na karshe kuwa, don hatta matan makwabta da kananan yara basu tsira ba

Wata mata mai suna Grace ta bayyana yadda mijinta mai dauke da cuta mai karya garkuwar jiki ya auri ‘yar su kuma suka hada kai wajen korarta daga gidanta.

Grace ta auri mijinta ne tun shekaru 18 da suka gabata kuma ba ta da burin da ya wuce su zauna lafiya da mijinta kuma aurensu ya dore.

Ta samu zantawa da wani gidan talabijin na kasar Kenya a ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairun 2020. Ta ce sun fara samun tangarda da mijinta ne tun bayan da ta samu labarin mijinta na lalata da diyarta.

Kwamacala: Mijina mai kanjamau ya auri 'ya ta, sun kuma hada baki sun kore ni daga gidan - Mata ta koka
Kwamacala: Mijina mai kanjamau ya auri 'ya ta, sun kuma hada baki sun kore ni daga gidan - Mata ta koka
Asali: Facebook

“Bayan tashin-tashina a gidan mai tarin yawa, mijina ya yanke shawarar auren diyata. Sun siyar da duk wasu filaye da kadarorin da muka mallaka sannan suka kore ni daga gidan. Sun gina gidansu mai kyau tare da diyata wacce daga bisani ya aura.,” Grace ta ce.

Mijinta ya sanar da ita cewa yana da damar auren diyarsu wacce suka ba ilimi har matakin jami’a tunda ba shi ya haifeta ba.

KU KARANTA: 'Yan kabilar Igbo sun Musulunta, sun kuma bayyana za su gabatar da bikin aurensu ta hanyar addinin Islama

“Sun haukata min karamin yarona mai shekaru uku, sun ba shi kwaya kuma tare da shi aka kore ni daga gidan. Ya yi min mugun duka tare da hana ni ko kayan sanyawa kafin in bar gidan. Ya ce bani da komai na isa gidan shi,” Grace ta sanar cikin kunar rai.

Kamar yadda Tuko.co.ke ta ruwaito, daya daga cikin abubuwan da suka sa Grace ta bar gidan shine, duk lokacin da wani ya mutu a yankin, mijinta na zuwa lalata da matansu. Idan kuwa tayi magana sai yace kishi ne kawai.

Bayan jure duk kalubalen da ta fuskanta, Grace ta yanke shawarar barin wa diyarta mijinta duk da ta gano yana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

“Na fara ganin katinan asibiti kuma bayan na karanta na gano yana dauke da HIV. Yana amfani da magunguna ne. Na yi gwaji daga baya kuma an ga bana dauke da cutar. Na bar gidan tare da karamar diyata wacce yayi kokarin yi mata fyade amma bai samu nasara ba,” ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng