Hukumar kwastam ta bankado miyagun hanyoyi 3 da ake safarar shinkafa Najeriya

Hukumar kwastam ta bankado miyagun hanyoyi 3 da ake safarar shinkafa Najeriya

Hukumar kwastam ta bayyana cewa sabbin dabarun da miyagun masu safarar kaya da fasa kauri suke amfani dasu wajen shigo da shinkafa shi ne yasa ake ganin haramtattun kayayyaki a cikin kasa.

Kaakakin hukumar kwastam, Joseph Attah ne ya bayyana haka cikin wata zantawa da yayi da kamfanin dillancin labarun Najeriya a Abuja a ranar Laraba, inda yace akwai abubuwa da dama dake sabbaba shigowa haramtattun kaya Najeriya duk da kokarin hukumar na hanawa.

KU KARANTA: Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya rasu yana da shekaru 112

Hukumar kwastam ta bankado miyagun hanyoyi 3 da ake safarar shinkafa Najeriya
Hukumar kwastam ta bankado miyagun hanyoyi 3 da ake safarar shinkafa Najeriya
Asali: Facebook

Attah yace yawancin masu fasa kauri suna amfani da boyayyun hanyoyi wajen shigo da kayayyakinsu sa’annan suna amfani da dabaru daban daban wajen boye kayan, ta haka suke shigo dasu.

“Mun ga yadda masu fasa kauri suke amfani da tulun iskar gas wajen shigo da haramtacciyar shinkafa bayan sun cikata fal da shinkafar, haka zalika wasu na amfani da tayoyin mota wajen shigo da shinkafa, wasu kuma na zuba buhunan shinkafa a cikin akwatin gawa wajen safararta zuwa Najeriya.

“Idan baka da tsarin leken asiri da tattara bayanan sirri babu yadda zaka gane wadannan dabarun, misali babu yadda zaka ga mutane tare da akwatin gawa kuma kace su bude maka ka gani idan dai ba wai ka samu bayanan sirri game dasu bane.

“Idan mutanen dake amfani da wannan dabaru sun samu nasarar shigo da shinkafar, shi ne sai ga kansu a kasuwani da shaguna da kuma gidajen jama’a ana amfani da su.” Inji shi.

Sai dai Attah yace manufar ayyukan yan fasa kauri shine yi ma tattalin arzikin kasa da tsaron kasa zagon kasa, amma yace ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajen yaki dasu har sai sun kawo karshen fasa kauri a kasar.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga manyan hafsoshin tsaron Najeriya da su samar da gudanar da cikakken nazari game da tsare tsare da dabarun da suke amfani dasu a yaki da ISWAP, don duba yiwuwar kirkiro sabbin dabaru.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng