‘Yan Boko Haram sun kama wasu Likitoci 3 a kasar Chad

‘Yan Boko Haram sun kama wasu Likitoci 3 a kasar Chad

Mun samu labari cewa Sojojin ‘Yan ta’addan Boko Haram da ke fada a karkashin Abubakar Shekau sun yi garkuwa da wasu mutane a kasar Chad.

Fitaccen ‘Dan Jaridar nan, Ahmed Salkida, shi ne ya bayyana wannan mummunan labari. Salkida ya bayyana wannan ne a kan shafinsa na Tuwita jiya.

Mista Ahmed Salkida ya ce ‘Yan ta’addan sun fitar da bidiyon da ke nuna cewa kama mutum uku a Chad. Wadannan mutane sun yi jawabi da Faransanci.

Salkida ya bayyana cewa wadanda aka kama sun roki shugaban kasar Chad, Idris Deby, ya kawo masu dauki daga hannun ‘Yan ta’addan na Boko Haram.

A cewar Salkida, wadannan mutane da kungiyar su ka kama, su na aiki ne a matsayin Malaman lafiya a yankin na tafkin Chad da ke kusa da Najeriya.

KU KARANTA: An zargi Sojojin Najeriya da zame kafa a lokacin harin Boko Haram

Rahotannin ba su iya bayyana lokacin da aka sace wadannan Malaman asibiti ba. Yanzu dai ‘Yan ta’addan su na bukatar a bada wani abu kafin su sake Ma’aikatan.

Ana tunanin cewa watakila Abubakar Shekau zai bukaci gwamnatin Chad ta saki Sojojinsa da aka kama, kuma har aka yanke masu hukuncin kisa a halin yanzu.

Haka zalikan, Ahmed Salkida ya bayyana cewa ‘Yan ta’addan za su ribatu da wadannan mutane da su ka kama, akalla ta hanyar daukarsu a matsayin Likitocin su.

Daga shekarar bara zuwa yanzu, kasar Chad ta na fuskantar mummunan kalubale wajen yaki da kungiyar ta’addan da ta addabi Yankin Sahara a Nahiyar Afrika.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel