Taron FEC ya hada NSA Munguno da Hadimin Shugaban kasa Kyari a Aso Villa

Taron FEC ya hada NSA Munguno da Hadimin Shugaban kasa Kyari a Aso Villa

A jiya Ranar Laraba, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta FEC wanda aka saba yi duk mako a cikin fadar shugaban kasa.

Ministocin Najeriya da-dama sun halarci wannan taro da ake kowace Ranar Laraba. Haka zalika manyan Hadiman shugaban kasa da ke da iko, sun halarci wannan zama.

Daga cikin Hadiman Buhari da aka gani a wajen wannan taro akwai Mai ba shugaban kasar shawara a kan harkar tsaro watau Babagana Munguno da COS Abba Kyari.

Ana zargin cewa ana samun sa-in-sa tsakanin Malam Abba Kyari wanda shi ne shugaban Ma’aikatan fadar gidan gwamnati da Janar Babagana Munguno mai ritaya.

Duka wadannan Hadimai su na cikin wadanda aka yi taron na jiya. Rahotanni sun bayyana cewa manyan gwamnatin kasar sun zauna kusa da juna ne a wajen wannan taro.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da manyan Sojoji ba tare da Monguno ba

Taron FEC ya hada NSA Munguno da Hadimin Shugaban kasa Kyari a Aso Villa
SGF, Osinbajo, Babagana Munguno da Abba Kyari a wani taro
Asali: Facebook

Wata Jaridar Najeriya ta rahoto cewa a lokacin da aka fara taron, kusan kujeru biyu ne tsakanin Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da kuma Malam Abba Kyari.

Daga baya da taro ya yi taro, Babagana Monguno ya matsa kusa da Abba Kyari. A lokacin da aka kare wannan taro, kujera daya ce kadai ta raba Monguno da Malam Kyari.

A cewar Jaridar, wanda ta zauna tsakanin Mai bada shawara kan harkar tsaron da Kyari ita ce sabuwar shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Misis Folasade Yemi-Esan.

A kwanakin baya, an samu labarin cewa Babagana Monguno ya rubutawa wasu manyan kasar wasika game da yadda Kyari ya ke shiga sharo babu shanu a gwamnatin Buhari.

A dalilin wannan ne wata jarida ta fara yada rade-radin cewa an hana Monguno shiga fadar shugaban kasa, bayan an yi wani taro da manyan hafsun Soji ba tare da shi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel