Hana bara a Kano: Malaman Tsangaya sun yi zazzafan martani ga Ganduje

Hana bara a Kano: Malaman Tsangaya sun yi zazzafan martani ga Ganduje

Babbar Kungiyar koli ta addinin Musulunci a jihar Kano, ta soki hukuncin gwamnatin jihar na haramta bara a kan titunan jihar da ta yi. Ta ce hakan bai dace ba kuma gwamnatin jihar ba ta dau lamarin ta yadda ya dace ba.

Wannan zancen na zuwa ne bayan gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya haramta bara a titunan jihar kwata-kwata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Ganduje a ranar Talata ya bada umarni, a cikin tsarin hade almajirai da kuma karatun dole na firamare da na sakandare na jihar, cewa kada a kara ganin wani almajiri yana bara a jihar.

Amma kuma yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, kungiyar malaman jihar Kano din karkashin shugabancin Sheikh Ibrahim Khaleel, ta bayyana cewa wannan matakin ba shi ya dace gwamnatin ta dauka ba.

Hana bara a Kano: Malaman Tsangaya sun yi zazzafan martani ga Ganduje
Hana bara a Kano: Malaman Tsangaya sun yi zazzafan martani ga Ganduje
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An bayyana dalilin da yasa 'yan kungiyar ISWAP suka kashe dan Mohammed Yusuf

Ya jaddada cewa akwai bukatar a tantance wanne irin bara ce aka haramta kuma a saka duk masu ruwa da tsaki a harkar kafin a kaddamar da ita.

Ya ce, “Don haramcin yayi aiki, akwai bukatar hadin kai tsakanin gwamnati da malaman tsangaya. Akwai bukatar tattaunawa, a gano kiyasin yawan yaran, dalilin hana bara da kuma sanin mutane nawa za a shigar. Akwai bukatar hada kai da wasu jihohi masu makwabtaka da jihar in har ana bukatar tabbatar lamarin.”

Sheikh Khaleel ya yi kira ga gwamnatin da ta tuntubi duk masu ruwa da tsaki da kuma malamai don samar da mafita mai dorewa wajen kashe bara kwata-kwata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel