Buhari ya kalubalanci manyan hafsoshin Soji su kirkiro sabbin dabarun yaki da Boko Haram

Buhari ya kalubalanci manyan hafsoshin Soji su kirkiro sabbin dabarun yaki da Boko Haram

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga manyan hafsoshin tsaron Najeriya da su samar da gudanar da cikakken nazari game da tsare tsare da dabarun da suke amfani dasu a yaki da ISWAP, don duba yiwuwar kirkiro sabbin dabaru.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito shugaba Buhari ya bayar da wannan umarni ne a yayin taron kara ma juna sani a kan harkar tsaro karo na 10 wanda tsofaffin daliban kwalejin tsaro ta kasa, AANDEC suka shirya a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba.

KU KARANTA: Yadda aka yi na zama sabon kaakakin majalisar dokokin jahar Kaduna – Zailani

Buhari ya kalubalanci manyan hafsoshin Soji su kirkiro sabbin dabarun yaki da Boko Haram
Buhari ya kalubalanci manyan hafsoshin Soji su kirkiro sabbin dabarun yaki da Boko Haram
Asali: Facebook

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan tsaro, Bashir Magashi ya bayyana cewa sabbin hare haren ta’addanci da ake samu yana faruwa sakamakon shan kayi da kungiyar ISIS ta yi a duniya, amma ya ce an baiwa hukumomin tsaro daman su shawo kan dukkanin wani nau’I na ta’addanci a kasar.

“Samuwar barbashin ISIS a yankin Afirka ta yamma babbar barazana ce a garemu, shi yasa muke hada kai da sauran kasashen Afirka da kungiyoyin kasa da kasa domin takaita wanzuwar ta’addanci tare da karya lagon yan ta’addan.

“Babu shakka Sojojinmu sun ci galaba a kan Boko Haram, kuma akwai bukatar su sake duba tsare tsaren don samun galaba a kan ISWAP dake kai hare hare a sassan kasar. Haka zalika suma masu satar mutane da garkuwa dasu muna gargadinsu su daina, ko kuma su fuskanci fushin hukuma domin kuwa an baiwa hukumomin tsaro izinin bin ta kansu.” Inji shi.

A nasa jawabin, shugaban AANDEC, Manjo Janar Garba Audu ya bayyana cewa sun shirya taron ne domin lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaro da ake fuskanta, inda yace taron zai mayar da hankali ne kan matsalolin dake addabar kasar nan kamar tattaunawa da masu garkuwa da yan bindiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel