Fusataccen soja ya harbe abokansa sojoji hudu, ya kashe kansa a Borno

Fusataccen soja ya harbe abokansa sojoji hudu, ya kashe kansa a Borno

Wani fusataccen soja ya budewa abokan aikinsa wuta a sansanin sojojin da ke Malam Fatori a jihar Borno. Tuni kuwa ya halaka hudu daga cikinsu, ya bar mutane biyu da munanan raunika sannan ya kashe kansa, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Sagir Musa, mai magana da yawun rundunar sojin, ya tabbatar da aukuwar mummunan lamarin. Ya ce hakan ya faru ne a sa’o’in farko na ranar Laraba.

Ya ce ana ta kokarin sanar da iyalan sojojin da lamarin ya ritsa da su sannan ana ci gaba da bincike.

Karin bayani na tafe...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel