Kuma dai: Gwamnatin Nasarawa ta hana bara kwata-kwata a jihar

Kuma dai: Gwamnatin Nasarawa ta hana bara kwata-kwata a jihar

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya haramta bara a titunan jihar. Ya sanar da hakan ne yayin rantsar da hukumar kare hakkin yara a Lafia a ranar Laraba.

Gwamnan ya ce, "ba tare da nuna gadara ba, wannan dokar ta hana bara a tituna kuma ta tanadi hukunci ga iyayen da suka watsar da nauyin da ke kansu. A don haka kuma, gwamnati ta dau matakin saka yaranmu da ke karatu a Tsangaya cikin karatun boko don magance wannan matsalar,"

Gwamna Sule ya ce tabbatar da dokar bada kariya ga yaran za ta tabbatar da tsaro, kiwon lafiyarsu da iliminsu don ci gaban jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yayi kira ga shugabannin gargajiya, addinai kuma da jama'a da su goyi bayan wannan salon.

Kuma dai: Gwamnatin Nassarawa ta hana bara kwata-kwata a jihar
Kuma dai: Gwamnatin Nassarawa ta hana bara kwata-kwata a jihar
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An bayyana dalilin da yasa 'yan kungiyar ISWAP suka kashe dan Mohammed Yusuf

A jawabin kwamishinan shari'a na jihar, Dr. Abdulkarim Kana, ya ce wannan dokar an kirkirota ne don matasa, jihar da kuma Najeriya baki daya.

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa, a kokarin tabbatar da ilimin firamare da sakandare kyauta a jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya haramta wa almajirai bara a titunan jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar da shirin ilimin farko ga kowa (BESDA) tare da raba shaidar daukar aiki ga malami 7,500 a jihar. Wannan na kunshe ne a takardar da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar ya fitar.

Kamar yadda gwamnan ya sanar, hada tsarin karatun almajiran da sabon tsarin zai tabbatar da toshe barakar bara a jihar gaba daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel