EFCC ta cafke shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano

EFCC ta cafke shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta kama tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano, wanda yanzu haka kuma shine shugaban marasa rinjaye na majalisar, Isiyaku Ali Danja, bisa zarginsa da cin mutuncin ofis da almundahanar kudaden aiyuka a mazabu.

A cikin jawabin da mukaddashin kakakin hukumar EFCC na kasa, Tony Orilade, ya fitar, ya bayyana cewa jami'an EFCC na ofishin Kano ne suka kama Danja ranar Talata biyo bayan samun wani korafi a kansa.

A cewar jawabin, an kama Danja ne bisa zarginsa da karkatar da makudan kudi, biliyan N1.5, da gwamnatin jihar Kano ta ware domin biyan wasu basukan haraji da hukumar tattara ta kasa (FIRS) ke bin jihar.

EFCC, ta bakin Orilade, ta bayyana cewa takardar korafin da suka karba ta nuna cewa Danja ya karkatar da kudaden daga asusun gwamnatin jihar Kano.

EFCC ta cafke shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano
Jami'an EFCC
Asali: Facebook

"Mun gano wasu asusu da aka tura wani kaso daga cikin adadin kudaden, daga cikin irin asusun da aka tura kudaden akwai na wani kamfani mai suna 'Allad Drilling Limited' da wanda ake zargi ne kadai keda ikon fitar da kudi daga asusun.

DUBA WANNAN: Hisbah ta kama wata mata da ke auren maza biyu a Kano

"Bincikenmu ya gano cewa wanda ake zargin ne ya dinga fitar da kudaden daga asusun," a cewar jawabin hukumar EFCC.

A kwanakin baya bayan nan ne hukumar EFCC ta cafke kwamishinan aiyuka na musamman a jihar Kano, Mukhtar Ishaq Yakasai, bisa zarginsa da karkatar da wasu makudan kudi a lokacin da yake shugabantar karamar hukumar Birnin Kano.

Orilade ya bayyana cewa hukumar EFCC zata gurfanar da Danja da Yakasai a gaban kotu da zarar ta kammala gudanar da bincike a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel