Na talauce na shiga tashin hankali bayan aurenta - Miji ya kira matarsa da mai farar kafa

Na talauce na shiga tashin hankali bayan aurenta - Miji ya kira matarsa da mai farar kafa

- Wani mutum wanda bai dade da yin aure ba yana neman shawara don zai saki matar shi

- Ya zargi matar shi da zama mayya don kuwa tun bayan aurensu komai nashi ya kare

- Shagon shi ya kone kurmus ga bashi da ake bin shi, kudin haya da abinci duka sun gagare shi

Wani mutum mai kokarin sakin matar shi ya ce yana zargin ta da zama mayya bayan duk kasuwancin shi ya fara tangarda bayan ya aureta.

A wallafar da aka yi a Nairaland, mutumin ya rubuta cewa kasuwancin shi na tafiya dai-dai kafin aurensu. Amma kuma shagon shi ya fara konewa daga nan talauci ya same shi. A halin yanzu kuwa da kyar yake cin abinci sau daya.

Kamar yadda ya wallafa, “Kafin in auri mata ta gaskiya kasuwanci na yana tafiya lafiya kalau. Ina da babban shago kuma ina samun kudi sosai. Ina iya siya wa kaina komai tare da daukar dawainiyar mahaifiyata da kannaina.

“Amma tun bayanda na yi aure a watannin biyu da suka gabata na fara ganin canji. Bayan kwana biyar da aure na shagona yayi gobara. Na rasa komai sannan ga shagon da ya kone dole in bada wani abu. Na samu wani karamin shago amma har yanzu bana samun wani abun kirki.”

KU KARANTA: Tashin hankali: A karon farko an samu mai cutar Coronavirus a nahiyar Afrika

Ya kara da cewa, “Akwai bashi mai yawa da mutane ke bi na kuma a halin yanzu ko abinci sau uku bamu iya ce. Na kasa biyan kudin hayar gida da na shagona don tuni muka koma gidan iyayena.

“Matata tana da ciki kuma za ta haihu a watan Afirulu amma har yanzu ba mu siya komai na jariri ba. Na yi dana-sanin taba saninta a rayuwata don ta kawo min karayar arziki. Ban tunkare ta da maganar ba saboda halin da take ciki. Amma gaskiya tana haihuwa zan sake ta. Zan karba wannan jaririn ta yadda za ta tafi da dan da ta haifa da wani kafin ta hadu da ni. Na tsaneta sosai kuma bana bukatarta.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel