Ku daina jiran masu arziki, ku auri wanda ya samu kuyi arzikin tare - Anita Joseph ta shawarci 'yan mata
- Wata ‘yar fim mai suna Anita Joseph wacce tayi aure a ranar masoya ta duniya ta yi babban kira ga ‘yan mata
- Ta bayyana jin dadinta da alfaharinta ta yadda ta fita daga cikin sahun ‘yan mata ta shiga na matar aure mai kaunar mijinta
- Ta shawarci ‘yan mata da su kiyayi jiran masu kudi don wasu ba alheri bane, zai fi idan suka auri talaka wanda zasu yi kudin tare
Wata ‘yar wasan kwaikwayo mai suna Anita Joseph wacce ta yi aure a ranar masoya ta duniya ta ba ‘yan mata shawara a kan su daina auren masu kudi. Su auri talaka wanda zasu yi kudin tare.
Kamar yadda ta wallafa:
“A gaskiya zan yi kewar rawar da nake yi don kuwa mijina ya ce min jikina yana da kyau kuma in daina rawa. Amma kuma na kan taba rawan a cikin dakina a ‘yan kwanakin nan.
“Mun yanke hukuncin yin aure a ranar masoya ta duniya ne saboda kaunar juna da muke yi. Mijina ya bani damar zabar ranar da nake so saboda kowa ya san biki na mata ne. Ina matukar farin cikin fita daga sahun ‘yan mata da ke kasuwa.” Ta ce.
Ta kara da cewa, “Mutane da yawa sun yi iyakar kokarinsu na ganin ban aure shi ba amma na ki saurararsu. Ko kafin mu fara soyayya na san akwai masu kushewa kuma sai da na shirya musu tsaf.
“Zan iya cewa na samu mijin da ke kaunata kuma ya fahimce ni. Don haka komai ya zo min da sauki tun 2017. Duk da ina da masoya da ke shirye don yi min komai, na dage a wajen shi don namiji daya ya ishe ni rayuwar farin ciki.
“Duk abinda nake so a namiji ina samu a wajen shi. Ban damu da sauran maza ba, shi kadai nake so.”
Joseph ta bukaci ‘yan mata da su nema abokan rayuwa sannan su yi hakuri da addu’a.
“Kada ku dinga bibiyar kudi. Idan kuka tsaya jiran mai kudi, ba dole bane ku samu. Mai kudin zai iya zama rashin alheri a tare da mace. Ubangiji zai iya so ki fara da farko ne, ku girma tare sannan ku tara tare da mijin,” ta ce.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng