EFCC: Muna bincikar kudin kamfen din Jonathan

EFCC: Muna bincikar kudin kamfen din Jonathan

Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, (EFCC) ta ce har yanzu tana bin diddigi a kan yadda aka samu kudin kamfen din tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Shehu Shu'aibu, mai bincike a EFCC, a ranar Talata ya sanar da hakan yayin da ake duba wata shari'a ta almundahanar kudade a babban kotun tarayya da ke Legas.

Ya ce wani kudi da ake zargin wani kamfani mai suna Joint Trust Dimensions Limited ya zuba a yayin kamfen din Jonathan din ana ci gaba da bincikarsa.

EFCC: Muna bincikar kudin kamfen din Jonathan
EFCC: Muna bincikar kudin kamfen din Jonathan
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Mai farin jini: Dubban jama'a sun yi tururuwar fitowa domin tarbar Buhari a Ondo (Hotuna)

Sauran wadanda ake zargin a cikin almundahanar N4.9bn din sun hada da Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama da kuma jami'an kungiyar yakin neman zaben Jonathan din sa suka hada da Nenadi Usman, tsohon ministan kudi da kema Yusuf Danjuma.

Ya bayyana kudaden da suka samu shiga cikin asusun bankin wannan kamfani.

Ya kara da cewa, "ban tabbatar da cewa kudaden na kamfen ne kadai ba. Har yanzu dai ana ci gaba da binciken wasu daga cikin kudaden da ake zargi."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kada Jonathan, wanda a shekarar yake neman zarcewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel