Babban sufetan Yansanda ya nemi Buhari ya basu bindigu 250,000 da motocin yaki 1000

Babban sufetan Yansanda ya nemi Buhari ya basu bindigu 250,000 da motocin yaki 1000

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bayyana cewa baya ga karancin jami’ai da rundunar take fama dasu, rundunar na bukatar karin bindigu guda 250,000 da motocin yaki samfurin APC guda 1,000 da alburusai da dama.

Punch ta ruwaito Adamu ya bayyana haka ne a ranar Talata, 25 ga watan Feburairu yayin zaman kwamitin majalisar wakilai dake kula da rundunar Yansandan Najeriya, wanda ya gudana da taken ‘Yadda za’a gyara rundunar Yansandan Njeriya.”

KU KARANTA: Tsuguni bata kare ba: EFCC ta tasa keyar ‘Mamar Boko Haram’ a kan zambar N42m

A jawabinsa, IG Adamu yace rundunar Yansanda na bukatar akalla barkonon tsohuwa da nakiyar hayaki guda miliyan 2, bindigun kwantar da tarzoma guda 200,000, na’urorin bin sawu guda 1000 da kuma jiragen leken asiri guda 770.

Haka zalika IG ya kara da cewa rashin tsarin albashi mai kyau ya sanya hazikan yan Najeriya masu kwakwalwa basu kaunar shiga aikin Dansanda, sai kuma matsalar wuraren zama masu kyau a barikin Yansanda da kuma karancin kasafin kudi.

A kokarinta na rage matsalolin dake addabar rundunar Yansandan Najeriya musamman matsalar karancin isassun jami’ai, hakan ne yasa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa rundunar daman daukan Yansanda 10,000.

Tun a ranar 23 ga watan Agusta na shekarar 2018 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sabon tsarin albashin Yansanda, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto Yansanda basu fara gani a kasa ba.

A wani labarin kuma, dakarun rundunar Sojojin Najeriya sun kashe babban Alkalin kungiyar ta’addanci na Boko Haram, Akalin Alkalai Muhammad Shuwa a yayin wani samame da suka kaddamar a yankin tafkin Chadi.

Wani bincike ya tabbatar da mutuwar akalla kwamandojin kungiyar guda 25 a cikin watanni biyu da suka gabata a sakamakon kara kaimi da wajen yaki da ta’addanci da rundunar Soji arewacin tafkin Chadi ta yi.

Wasu majiyoyi sun bayyana ma jaridar PRNigeria cewa yan ta’adda da daman a ta arcewa zuwa cikin kasashen Chadi, Nijar da Kamaru sakamakon mace mace da ake yawan samu a sansanonin Boko Haram a dalilin bamabamai da suke binnewa a zagaye da sansanonin, musamman bayan harin jiragen Soji.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel