Tsuguni bata kare ba: EFCC ta tasa keyar ‘Mamar Boko Haram’ a kan zambar N42m

Tsuguni bata kare ba: EFCC ta tasa keyar ‘Mamar Boko Haram’ a kan zambar N42m

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta gurfanar da Hajiya Aisha Wakili wanda aka fi sani da suna Mamar Boko Haram akan zarginta da laifi zamba na naira miliyan 42.

KU KARANTA: Hukumar NECO ta sallami ma’aikata 19 masu amfani da takardun karatu na bogi

Hukumar EFCC reshen jahar Borno ce ta gurfanar da Aisha tare da Saidu Daura, Lawal Shoyade da Adamu Sani a gaban Alkalin babbar kotun tarayya dake garin Maiduguri, Mai Sharia Dagat, inji rahoton jaridar TheCable.

Tsuguni bata kare ba: EFCC ta tasa keyar ‘Mamar Boko Haram’ a kan zambar N42m
Aisha Alkali
Asali: Facebook

EFCC na zargin mutanen hudu ne da laifin hadin baki wajen zambar naira miliyan 42 a lokacin da suke aiki tare da wata kungiya mai zaman kanta dake bayar da agaji, a garin Maidugurin jahar Borno.

“Ke Aisha Alkali Wakili, Tahiru Alhaji Saidu Daura, Yarima Lawal Shoyade, a lokacin da ki ke shugabar gidauniyar Complete Care and Aid da kuma Sani Mallam Adamu na kamfanin Sani Smart Globar Ventures, a tsakanin ranar 23 ga watan Oktobar 2018 da 5 ga watan Nuwambar 2018 kun yaudari Bukar Kachallah na kamfanin Abks Ventures Nig Ltd kudi naira miliyan 42.

“Kun damfareshi kudaden ne da sunan kun aiwatar da kwangilar kawo wake alhali kun san karya ne, wanda hakan ya saba ma sashi na 1(1)(b) na dokokin yaki da damfara na shekarar 2006 wanda hukuncinsa ke kunce a sashi 1(3) na kundin.” Inji takardar karar.

Sai dai Aisha ta musanta aikata laifin, daga nan sai Alkalin kotun ya bayar da umarnin a garzaya da Aisha da sauran mutanen zuwa gidan yari har zuwa ranar 27 ga watan Feburairu da zai saurari bukatar bayar da belinsu.

Wannan sabon kamu ya faru ne bayan kimanin wata guda da aka gurfanar da ita a kan zambar naira miliyan 111.

A wani labarin kuma, wata babbar kotun majistri dake zamanta a jahar Kano a karkashin jagorancin Alkali Aminu Gabari ta bayar da beli ga mutumin da ake tuhuma da kitsawa tare da watsa labarin auren shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministocinsa Sadiya Umar Farouk da Zainab Shamsuna.

Ana thumar mutumin mai suna Kabiru Muhammad dan shekara 32 ne laifin kirkirar labarin karya game da auren shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministar kudi Zainab Ahmad da kuma ministar kula da yan gudun hijira, Sadiya Umar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng