Kotu ta bayar da belin mutumin da ya kitsa labarin auren Buhari da ministocinsa 2
Wata babbar kotun majistri dake zamanta a jahar Kano a karkashin jagorancin Alkali Aminu Gabari ta bayar da beli ga mutumin da ake tuhuma da kitsawa tare da watsa labarin auren shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministocinsa Sadiya Umar Farouk da Zainab Shamsuna.
Daily Trust ta ruwaito ana thumar mutumin mai suna Kabiru Muhammad dan shekara 32 ne laifin kirkirar labarin karya game da auren shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministar kudi Zainab Ahmad da kuma ministar kula da yan gudun hijira, Sadiya Umar.
KU KARANTA: Hukumar NECO ta sallami ma’aikata 19 masu amfani da takardun karatu na bogi
Da fari dai Kabiru wanda mazaunin unguwar Kurna Layin Magani ne yana hannun jami’an hukumar DSS reshen jahar Kano ne bayan bayyanarsa ta farko a gaban kotu a ranar 10 ga watan Oktoba inda aka tuhume shi da lafin batanci da kazafi.
An shaida ma kotun cewa abin da Kabiru ya yi ka iya kawo rudani, tare da bata ma mutanen daya shafa suna, da kuma kunna wutar rikici a tsakanin iyalansu. Koda aka karanto masa tuhume tuhumensa, Kabiru ya amsa su duka.
Ganin haka yasa Alkali Gabari ya bayar da belinsa a kan kudi naira miliyan 1, da mutane biyu da zasu tsaya masa, wanda dole ne daya daga cikinsu ya kasance shugaba ko sakataren kungiyar yan kasuwan Singer daya kuma jami’in gwamnati daya kai mataki na 15 a aiki.
Daga karshe Alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Maris.
A wani labarin kuma. kwamitin gudanarwa ta hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandari a Najeriya, NECO ta amince da fatattakar wasu ma’aikatan hukumar 19 da aka samu suna amfani da takardun karatu na bogi.
Shugaban sashin watsa labaru da hulda da jama’a na hukumar, Azeez Sani ne ya bayyana haka inda yace kwamitin tantance ma’aikata da hukumar ta kafa ne ta bankado wadannan mutane.
Sani ya ce yadda aikin kwamitin ya gudana shi ne ta gayyaci wasu ma’aikatan hukumar da ake zarginsu da amfani da shaidun kammala karatu na bogi, inda suka amsa tambayoyi daga wajenta, kuma a nan ne suka tabbatar da rashin ingancin takardunsu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng