Ban ci kudin kowa ba, bita-da-kulli kurum ake ta yi mani saboda siyasa - Galadima

Ban ci kudin kowa ba, bita-da-kulli kurum ake ta yi mani saboda siyasa - Galadima

Injiniya Buba Galadima wanda gwamnatin Najeriya ta karbe masa gidaje da kamfanoni, ya bayyana cewa bita-da-kulli ce ake yi masa saboda ya koma bangaren hamayya.

Buba Galadima ya yi magana da gidan Jaridar BBC Hausa inda ya shaida cewa bai karbi kudin kowa ba. Tsohon Sakataren jam’iyyar CPC na kasa, ya koka da wannnan lamari.

A cewarsa, kwangilar shigo da takin zamani aka ba shi a lokacin gwamnatin Ibrahim Shekarau a 2003, amma Galadima y ace bai yi nasarar samun kudin da zai yi wannan aiki ba.

‘Yan kasuwa sun hana ‘Dan siyasar kayan da ya bukata ne saboda hukumomin FBI na kasar Amurka su na binciken wannan banki wanda a karshe ya narke a cikin Unity Bank.

Duk da Galadima bai yi sa’ar shigo da kayan ba, daga baya an fito an bayyana masa cewa kudin ruwa ya taru daga bashin da ya bukaci ya karba, ko kudin ba su shigo hannunsa ba.

Injiniya Galadima ya shaidawa ‘Yan jarida cewa an kai shi kotun tarayya domin a tursasa masa ya biya wannan kudin ruwa na Miliyan 349, kuma Alkali ya bada hukuncin ayi haka.

KU KARANTA: Buba Galadima ya rasa gida da kamfaninsa a hannun AMCON

Ban ci kudin kowa ba, bita-da-kulli kurum ake ta yi mani saboda siyasa - Galadima
Buba Galadima ya ce zai kai hukumar AMCON kotu
Asali: UGC

Sai dai kuma daga baya fitaccen ‘Dan adawar ya daukaka shari’a, ya tafi gaban kotun daukaka kara, inda kuma Alkalai su ka ba shi gaskiya a shekarar bara, kuma maganar ta mutu.

Kwatsam sai kuma yanzu hukumar AMCON ta koma wajen wani karamin kotu, ta samo iznin korar tsohon Aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari daga gidan da ya ke zama.

“Ni ya kamata a biya kudi domin saboda a dalilin matsalar bankinsu aka hana ni shigo da kayan. Da watakila yanzu na kai Dangote, ko Dantata ko Abdussamadu kudi.” Inji Injiniyan.

Gawurtaccen ‘Dan siyasar ya ce ko da za a sama sa bindiga ba zai sauka daga akidarsa ba. Ya ce watakila su kwana a titi, domin jama’a su ga irin Fir’aunanci da ake yi a Najeriya.

Injiniya Buba Galadima ya ce watakila silar arzikinsa ce ta zo a sakamakon wannan sa-in-sa. Galadima ya ce yanzu zai bukaci diyya a hannun hukumar AMCON a gaban kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel