APC: Shugaban karamar hukuma da kansilolinsa 10 sun koma PDP a Zamfara

APC: Shugaban karamar hukuma da kansilolinsa 10 sun koma PDP a Zamfara

A ranar Litinin ne shugaban karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara, Aminu Mudi ya sanar da sauya shekarsa daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar. An zabi Mudi ne kusan shekara daya da ta gabata karkashin jam'iyyar APC tare da kansiloli goma.

Ya ce komawarsa jam'iyyar ta biyo bayan hukuncin da majalisar zababbunsa ta bayyana na barin jam'iyyar da ta kawo su matsayinsu.

"Mun matukar gamsuwa cewa gwamnatin PDP din karkashin Alhaji Bello Matawalle tana kokari wajen tabbatar da ci gaban jihar mu.

"Gwamnan ya matukar yin kokari wajen dawo da zaman lafiya ga yankunan jihar ballantana kauyuka inda noma da sauran kasuwanci suka gagara a shekarun baya.

APC: Shugaban karamar hukuma da kansilolinsa 10 sun koma PDP a Zamfara
APC: Shugaban karamar hukuma da kansilolinsa 10 sun koma PDP a Zamfara
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Abinda yasa NSA Monguno bai halarci taron Buhari da shugabannin hukumomin tsaro ba

"A matsayinmu na masu son ci gaba da zaman lafiya a jihar mu, mun zauna tare da duba kokarinsa tare da mabiyansa inda muka yanke hukuncin shiga cikinsu don kawo canji na gari," shugaban karamar hukumar ya bayyana.

A yayin karbar masu sauya shekar, Matawalle ya nuna farin cikinsa a kan hukuncinsu. "Ina da tabbacin cewa jam'iyyarmu za ta ci gaba da karbar jama'a daga jam'iyyu daban-daban na jihar nan saboda kokarin kawo romon damokaradiyya da muke yi.

"Ina so in sanar da cewa kofa bude take ga kowa mai son ganin ci gaban jiharmu. Ga wadanda basu dade da komowa jam'iyyar ba, ku sani cewa zamu baku dama kamar sauran mambobin jam'iyyar," ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel